Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shawara A Kan Yin Nazari

Shawara A Kan Yin Nazari

Yadda Za Mu Yi Amfani da Sashen “Duba Sabon Abu” da Kyau

Sashen “Duba Sabon Abu” da ke JW Library® da jw.org yana ɗauke da littattafai da kuma bidiyoyin da aka wallafa kwana-kwanan nan. Ta yaya za ka yi amfani da sashen nan don ka ga sabbin abubuwan da aka fitar?

JW Library

  • Akan fitar da kowane talifi ta wajen saka shi a ƙarƙashin jerin talifofin da ya dace da shi. Don haka, idan jerin talifofi suka bayyana a sashen “Duba Sabon Abu,” za ka iya sauƙar da shi. Sai ka karanta talifi na farko a cikin jerin talifofi wanda aka jera su bisa ga kwanan watan da aka fitar da su.

  • Ba za ka iya karanta littattafai masu tsawo kamar mujallu a lokaci ɗaya ba. Kana iya saka irin littattafan nan a sashen “Favorites” don ya yi maka sauƙi ka ga littafin kuma ka ci gaba da karatun. Idan ka gama karatun, za ka iya cire shi daga sashen “Favorites.”

JW.ORG

Wasu bayanai har da labarai da kuma sanarwa suna fitowa ne kawai a dandalin jw.org ba a JW Library ba. Ka riƙa duba sashen nan “Duba Sabon Abu” don ka ga talifofin da aka fitar a kwana-kwanan nan.