Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin, gyara ƙwayoyin halitta ya yi maganin tsufa?

Ana Ƙoƙarin Ƙara Tsawon Rayuwa

Ana Ƙoƙarin Ƙara Tsawon Rayuwa

“Na ga hidimar da Allah ya ba wa mutane su yi ta yi. Ya yi kowane abu da kyau a daidai lokacinsa. Ban da haka ma, ya sa burin yin rayuwa har abada a zuciyar ’yan Adam.”​Mai-Wa’azi 3:​10, 11, New World Translation.

ABIN da aka ambata a sama kalaman wani sarki mai hikima ne mai suna Sulemanu kuma sun nuna yadda ’yan Adam suke ji game da rayuwa. Mutane sun daɗe suna ƙoƙari su ƙara tsawon rayuwarsu domin rayuwa ba ta jimawa kuma mutuwa ta addabi mutane. Akwai tatsuniyoyi da yawa a kan yadda mutane suka yi ƙoƙarin samun abin da zai ƙara tsawon rayuwarsu.

Alal misali, mutane kamar Gilgamesh, wani sarkin yankin Sumer. Akwai tatsuniyoyi da dama da aka bayar game da rayuwarsa. Ɗaya daga cikin tatsuniyoyin shi ne “Epic of Gilgamesh.” A cikin tatsuniyar, an ce ya yi wata tafiya mai ban tsoro don ya nemi abin da zai hana shi mutuwa. Amma ƙoƙarinsa ya ci tura.

Wani matsafi mai bincike na zamanin dā a ɗakin bincikensa

Wajen shekaru 2000 kafin a haifi Yesu, wasu masu bincike a ƙasar China sun haɗa wani ruwan tsafi da aka yi imanin cewa zai iya sa mutane su rayu har abada. Sun haɗa sinadiran da ake kira mercury da arsenic. Ana ganin wannan haɗin ne ya jawo mutuwar manyan sarakuna da yawa a China. Tsakanin shekara ta 500 zuwa 1500 bayan haihuwar Yesu, wasu matsafa masu bincike a Turai sun yi ƙoƙari su mai da zinariya ta zama yadda jikin ɗan Adam zai iya narƙar da ita. A ganinsu, da yake zinariya ba ta koɗewa, shan zinariyar nan zai iya ƙara tsawon ran ɗan Adam.

A yau, wasu ’yan kimiyya da suke nazarin halittu masu rai da masu nazarin yadda ake gadan ɗabi’u suna ƙoƙari su gano abin da yake sa mutane tsufa. Kamar matsafa masu bincike na dā, su ma sun nuna cewa har wa yau mutane sun damu da batun tsufa da mutuwa. Amma haƙarsu ta cim ma ruwa kuwa?

ALLAH “YA SA BURIN YIN RAYUWA HAR ABADA A ZUCIYAR ’YAN ADAM.”​—MAI-WA’AZI 3:​10, 11NW

BINCIKE A KAN ABIN DA KE SA MUTANE TSUFA

’Yan kimiyya masu nazarin ƙwayar halitta sun ba da bayanai dabam-dabam da suka fi 300, a kan abin da ya sa muke tsufa da kuma mutuwa. A shekarun baya-bayan nan, wasu daga cikinsu sun sarrafa ƙwayoyin halitta da sinadarai masu gina jiki don su hana mutane da dabbobi tsufa da wuri. Hakan ya sa wasu masu arziki sun ba da kuɗi don a ƙara bincike a kan abin da yake jawo mutuwa. Mene ne ’yan kimiyya suka yi?

Yadda ake ƙoƙarin ƙara tsawon rai. Wasu masu nazarin halittu masu rai suna ganin muna tsufa ne domin abin da ke faruwa da wani sashen ƙwayar halittarmu da ake kira telomere. A duk lokacin da ƙwayoyin halitta suke rabuwa, wannan sashen ne yake kāre bayanai game da ɗabi’un da ’ya’ya suke gāda daga jikin iyayensu. Amma a duk lokacin da ƙwayoyin halitta suka hayayyafa, wannan sashen yana raguwa. Kuma a ƙarshe, ƙwayoyin za su daina hayayyafa, sa’an nan mutum ya soma tsufa.

A shekara ta 2009, Elizabeth Blackburn, wata ’yar kimiyya mai lambar yabo ta Nobel, tare da abokan aikinta sun gano wani sinadarin da yake hana telomere raguwa da wuri, don a jinkirta tsufa. Sai dai masu binciken sun ce ko da sashen ƙwayar halittar nan bai ragu ba, babu tabbaci cewa za mu wuce shekaru 70 ko 80.

Gyara ƙwayoyin halitta wata hanya ce kuma na magance matsalar tsufa. Bayan ƙwayoyin halittarmu sun tsufa kuma sun daina hayayyafa, sukan rikitar da ƙwayoyin halittar da ke kāre lafiyar jikinmu. Hakan yana jawo kumburin wani sashen jiki da ciwon gaɓoɓi da dai wasu cututtuka. A kwanan nan, ’yan kimiyya a Faransa sun gyara wasu ƙwayoyin halitta da aka samo daga jikin wasu tsofaffi, a ciki har da mutanen da suka fi shekara 100. Shugaban masu binciken, wato, Farfesa Jean-Marc Lemaître, ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa “zai yiwu a sa [ƙwayoyin halitta] su dawo yadda suke kafin suka tsufa.”

SHIN, ’YAN KIMIYYA ZA SU IYA ƘARA TSAWON RANMU?

Wasu ’yan kimiyya ba su yarda cewa maganin jinkirta tsufa zai iya ƙara tsawon ran ɗan Adam fiye da yadda yake a yau ba. Hakika, tsawon rayuwar ɗan Adam ya ɗan ƙaru tun daga ƙarni na 19 a zamaninmu. Amma hakan ya yiwu ne domin wasu magunguna da rigakafi da kuma nasarar da aka samu a yaƙar wasu cututtuka. Ƙari ga haka, mutane da dama sun koyi kasancewa da tsabta. Wasu ’yan kimiyya sun yarda cewa tsawon ran ɗan Adam ba zai iya ya fi yadda yake a yau ba.

Wajen shekaru 3,500 da suka shige, wani marubucin Littafi Mai Tsarki mai suna Musa ya rubuta cewa: “Tsawon kwanakinmu a duniya dai saba’in ne, ko tamanin, in mun sami ƙarfi. Duk da haka, tsawonsu fama ne tare da wahala, sukan wuce da sauri, tamu kuwa ta ƙāre.” (Zabura 90:10) Duk da ƙoƙarin da ’yan Adam suke yi su ƙara tsawon rayuwarsu, rayuwa tana nan kamar yadda Musa ya kwatanta ta.

Akasin haka, wasu dabbobi suna rayuwa na ɗarurruwan shekaru, kuma wasu itatuwa kamar itacen kuka sukan kai shekaru dubbai. Hakika, a duk lokacin da muka gwada tsawon rayuwarmu da na irin halittun nan, hakan zai iya sa mu tambayi kanmu cewa, ‘Shin, Allah ya nufe mu da yin rayuwa na tsawon shekaru 70 ko 80 ne kawai?’