Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

HASUMIYAR TSARO Na 1 2023 | Lafiyar Kwakwalwa​—Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka?

A duk faɗin duniya, miliyoyin mutane suna fama da matsalar ƙwaƙwalwa. Manya da yara, ko da yaya matsayinsu yake ko iliminsu ko addininsu ko daga ina ne suka fito, dukansu suna iya fama da ciwon nan. Me ake nufi da matsalar ƙwaƙwalwa kuma ta yaya take shafan mutane? A wannan mujallar, za a tattauna muhimmancin neman taimako daga asibiti idan mutum yana fama da ciwon nan da kuma yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimakawa a hanyoyi da dama.

 

Matsalar Ƙwaƙwalwa a Faɗin Duniya

Matsalar kwakwalwa za ta iya shafan kowa ko da manya ne ko yara ko da daga ina ne suka fito. Za ka ga yadda shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka idan kana fama da matsalar kwakwalwa.

Allah Ya Damu da Kai

Me ya sa kake da tabbaci cewa Jehobah ya fahimci yadda kake ji fiye da kowa?

1 | Adduꞌa​—“Ku Danka Masa Dukan Damuwarku”

Za ka iya yin adduꞌa game da duk wani abu da ke damunka kuwa? Ta yaya yin adduꞌa zai taimaka ma wadanda suke fama da tsananin damuwa?

2 | “Karfafa Daga Kalmar Allah”

Sakon da ke Littafi Mai Tsarki ya sa mu kasance da bege cewa nan ba da dadewa za a kawar da dukan abubuwan da ke sa mu bakin ciki.

3 | Taimako Daga Mutane da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki

Labaran mutane kamar mu da aka ambata a Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu san cewa ba mu kadai ba ne saꞌad da muke fama da tsananin damuwa.

4 | Za Mu Sami Shawara Mai Kyau a Cikin Littafi Mai Tsarki

Ka ga yadda yin tunani a kan Ayoyin Littafi Mai Tsarki da kuma kafa makasudai za su taimaka mana idan muna fama da matsalar kwakwalwa.

Yadda Za A Taimaka Wa Masu Fama da Matsalar Kwakwalwa

Idan ka taimaka wa abokinka da ke fama da matsalar kwakwalwa hakan zai amfane shi.