Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TARIHI

Na Sami Albarka a Yin Aiki da Mutanen da Suka Manyanta

Na Sami Albarka a Yin Aiki da Mutanen da Suka Manyanta

A TSAKANIN shekara ta 1935 zuwa 1937 ne iyayena James da Jessie Sinclair suka koma wata ƙaramar hukuma da ake kiran Bronx a wani birni da ke jihar New York. Sun sami wani aboki mai suna Willie Sneddon da ya ƙauro daga ƙasar Scotland kamar iyayena. Cikin ’yan mintoci da suka haɗu da juna sai su uku suka fara hira game da iyalansu. Hakan ya faru wasu shekaru kafin a haife ni.

Mahaifiyata ta gaya ma Willie cewa kafin Yaƙin Duniya na Ɗaya, babanta da ’yayanta sun mutu a ruwa sa’ad da kwalekwalen da suke kama kifi da shi ya bugi mahaƙar kuza a Tekun Arewa. Willie ya ce, “Babanki yana Jahannama!” Me ya sa Willie ya yi wannan furucin? Domin shi Mashaidin Jehobah ne. Kuma mahaifiyata ta yi mamaki sosai don haka sai ta soma nazari.

Willie da Liz Sneddon

Abin da Willie ya faɗa ya ɓata wa mahaifiyata rai domin ta san cewa mahaifinta mutumin kirki ne. Amma Willie ya ƙara cewa, “Kin sa cewa Yesu ma ya je jahannama?” Sai mahaifiyata ta tuna wani koyarwar coci na asali da ya ce Yesu ya je jahannama kuma aka ta da shi bayan kwana uku. Hakan ya sa ta soma tunani. ‘Idan jahannama wuri ne da ake gana wa mutane azaba a cikin wuta, me ya sa aka tura Yesu wurin?’ Wannan ya sa mahaifiyata ta soma son Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ta soma halartan taro a Ikilisiyar Bronx kuma aka yi mata baftisma a shekara ta 1940.

Da ni da mahaifiyata, daga baya da mahaifina

A wannan lokacin, ba a ƙarfafa iyaye su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da yaransu. Sa’ad da nake jariri, mahaifina ne yake kula da ni sa’ad da mahaifiyata ta tafi taro da kuma wa’azi a ƙarshen mako. Bayan wasu shekaru, sai ni da shi muka soma halartan taro da mahaifiyata. Tana ƙwazo a wa’azi kuma tana nazari da mutane da yawa. Akwai lokacin da ta tara ɗalibanta suna nazari tare don suna zama kusa da juna. Ni kuma nakan bi ta wa’azi a lokacin da muka samu hutu a makaranta. Ta hakan ne na koya game da Littafi Mai Tsarki da kuma yadda zan koya wa mutane abin da ke ciki.

A gaskiya, sa’ad da nake yaro, ban ɗauki bauta wa Jehobah da muhimmanci ba, ina  yi ne kawai. Amma sa’ad da nake ɗan shekara 12, sai na zama mai shelar Mulki kuma tun daga lokacin nakan fita wa’azi a kai a kai. Na tsai da shawarar bauta wa Jehobah sa’ad da nake ɗan shekara 16, kuma na yi baftisma a ranar 24 ga Yuli 1954 a taron yanki da aka yi a birnin Toronto a ƙasar Kanada.

HIDIMA A BETHEL

Wasu ’yan’uwa da ke ikilisiyarmu suna Bethel a dā. Sun ƙarfafa ni sosai. Yadda suke ba da jawabi da kuma bayyana koyarwar Littafi Mai Tsarki ya burge ni sosai. Makasudina shi ne zuwa Bethel ko da yake malaman makarantarmu suna so in je jami’a. Saboda haka, na cika fam na zuwa Bethel a wannan taron yanki da aka yi a birnin Toronto. Na sake yin hakan a shekara ta 1955 a taron da aka yi filin wasa da ke Yankee a birnin New York. Ba da daɗewa ba, sa’ad da nake shekara 17, sai na samu wasiƙar soma hidima a Bethel da ke Brooklyn a ranar 19 ga Satumba, 1955. Na soma aiki a wurin da ake haɗa littattafai da ke 117 Adams Street a rana ta biyu da na soma hidima a Bethel. Ba da daɗewa ba, sai na soma aiki da na’urar da ke shirya littattafai masu shafi 32 don a kai su wurin wata na’ura da za ta ɗinka su.

Na soma hidima a Bethel da ke Brooklyn sa’ad da nake ɗan shekara 17

Bayan na yi wata guda a wurin da ake haɗa littattafai, sai aka tura ni Sashen Mujallu don na iya yin amfani da tafireta. A wannan lokacin, ’yan’uwa suna amfani da tafireta don su rubuta adireshin waɗanda suke son karanta Hasumiyar Tsaro da Awake! a kan wani irin takarda na musamman. Bayan wasu watanni, na soma aiki a Sashen Aika Littattafai. Ɗan’uwa Klaus Jensen da ke kula da wannan sashen ya tambaye ni ko zan so in bi direban da ke kai littattafai zuwa gaɓar teku don a tura su faɗin duniya. Ƙari ga haka, akwai buhunan mujallu da za a kai gidan waya don a  tura wa ikilisiyoyi da ke Amirka. Ɗan’uwa Jensen ya ce yin wannan aiki zai taimaka mini sosai. A lokacin nauyin jikina wajen kilo 57 ne kuma na yi siriri sosai. Waɗannan tafiye-tafiye zuwa gaɓar teku da gidan waya ya taimaka mini na samu ƙarfin jiki. Babu shakka, Ɗan’uwa Jensen ya san cewa hakan zai iya taimaka mini!

Ban da haka ma, waɗanda suke Sashen Mujallu suna tura mujallu zuwa ikilisiyoyi. Ta hakan ne na san cewa ana buga mujallunmu a Brooklyn cikin harsuna dabam-dabam kuma a tura zuwa wasu ɓangarorin duniya. Ban taɓa ji game da waɗannan harsuna ba amma ina farin ciki cewa ana tura dubban mujallu zuwa wurare masu nisa a duniya. Kuma a lokacin ban san cewa zan samu gatan ziyarar waɗannan wurare a nan gaba ba.

Ni da Robert Wallen da Charles Molohan, da Don Adams

A shekara ta 1961, an tura ni yin aiki a Sashen Kuɗi kuma Ɗan’uwa Grant Suiter ne ke kula da wannan sashen. Bayan wasu shekaru, sai Ɗan’uwa Nathan Knorr ya kira ni zuwa ofishinsa, shi ne ke kula da aikinmu a faɗin duniya a lokacin. Sai ya ce wani Ɗan’uwa da ke aiki tare da shi zai halarci Makarantar Hidima ta Mulki na wata ɗaya kuma bayan haka, zai yi aiki a Sashen Hidima. Zan ɗauki matsayinsa kuma na yi aiki tare da Ɗan’uwa Don Adams. Kuma Ɗan’uwa Don ne ya karɓi fam na Bethel da na cika a taron yanki da aka yi a shekara ta 1955. ’Yan’uwa biyu masu suna Robert Wallen da Charles Molohan suna aiki a wurin. Kuma mu huɗu mun yi aiki tare fiye da shekara 50. Na yi farin ciki sosai da na yi aiki da waɗannan maza da suka manyanta.​—Zab. 133:1.

Ziyarata ta farko a ƙasar Venezuela a shekara ta 1970

 A shekara ta 1970 ne na soma ziyarar ofisoshin Shaidun Jehobah dabam-dabam na ’yan makonni a kowace shekara ko bayan shekara biyu. A wannan ziyarar, nakan ƙarfafa waɗanda suke hidima a Bethel da masu wa’azi a ƙasashen waje a faɗin duniya kuma ina duba fayil na rahoton ayyukan ofisoshin da na kai musu ziyara. Ƙari ga haka, na yi farin cikin haɗuwa da waɗanda suka sauke karatu daga Makarantar Gilead a dā kuma har ila suna hidimarsu da aminci! Na sami gatar ziyarar ƙasashe fiye da 90 kuma na yi farin cikin yin hakan.

Na yi farin cikin ziyarar da na kai wa ’yan’uwa a fiye da ƙasashe 90!

NA SAMI ABOKIYA MAI IBADA SOSAI

An tura dukan waɗanda suke hidima a Bethel da ke Brooklyn zuwa ikilisiyoyi da ke wuraren birnin New York. An tura ni ikilisiyar da ke ƙaramar hukumar Bronx. An sami ƙaruwa sosai a ikilisiya ta farko da ke wannan hukumar kuma aka raba ta. Sai aka soma kiran ikilisiya ta farkon, Upper Bronx, kuma a wannan ikilisiyar nake.

A tsakanin shekara ta 1965 zuwa 1967 wata iyalin ’yan Latvia da suka soma bauta wa Jehobah a Bronx ta kudu suka ƙauro zuwa yankin ikilisiyar da nake. Livija ’yarsu ta fari ta soma hidimar majagaba ta kullum nan da nan bayan ta gama makarantar sakandare. Bayan ’yan watanni ta ƙaura zuwa jihar Massachusetts don ta yi hidima a inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai. Sai na soma rubuta mata wasiƙa ina ba ta labarin ikilisiyar, ita kuma tana gaya min yadda take nasara a hidimarta a yankin birnin Boston.

Ni da Livija

Bayan wasu shekaru, Livija ta soma hidimar majagaba ta musamman. Da yake tana so ta ƙara ƙwazo a hidimarta ga Jehobah, sai ta cika fam na zuwa Bethel kuma aka gayyace ta a shekara ta 1971. Kamar dai Jehobah ya sauko mini da wahayi! Kuma a ranar 27 ga Oktoba na shekara ta 1973 muka yi aure kuma Ɗan’uwa Knorr ne ya ba da jawabin aurenmu. Misalai 18:22 ta ce: “Wanda ya sami mata [mai hankali], abin kirki ya samu, yana kuwa samun alheri wurin Ubangiji.” Ni da Livija mun yi farin cikin yin hidima a Bethel fiye da shekara 40. Kuma har ila muna ikilisiya da ke yankin Bronx.

NA YI AIKI DA ’YAN’UWAN KRISTI

Yin aiki da Ɗan’uwa Knorr ya sa ni farin ciki sosai. Yana aiki da ƙwazo kuma yana son masu wa’azi a ƙasashen waje don aikin da suke yi a faɗin duniya. Da yawa a cikinsu ne Shaidu na farko a ƙasashen da aka tura su hidima. Na yi baƙin ciki sosai sa’ad da Ɗan’uwa Knorr ya soma ciwon kansa a shekara ta 1976. Akwai lokacin da ba ya iya tashi daga gadonsa, sai ya ce in karanta wasu abubuwan da ake so a buga. Kuma ya ce in kira Ɗan’uwa Frederick Franz don ya saurari abin da nake karantawa. Daga baya na gano cewa domin Ɗan’uwa Franz ba ya gani da kyau ne ya sa Ɗan’uwa Knorr yake karanta masa abubuwan da ake so a wallafa.

Sa’ad da ni da Daniel da Marina Sydlik muka kai ziyara a wata ƙasa a shekara ta 1977

 Ɗan’uwa Knorr ya mutu a shekara ta 1977, kuma waɗanda suka san shi kuma suna ƙaunarsa sun sami ƙarfafa don ya gama hidimarsa a duniya da aminci. (R. Yoh. 2:10) Bayan haka, sai Ɗan’uwa Franz ya soma ja-gorancin aikin wa’azin da ake yi a faɗin duniya.

A wannan lokacin, na zama sakataren Ɗan’uwa Milton Henschel wanda ya yi aiki tare da Ɗan’uwa Knorr shekaru da yawa. Ɗan’uwa Henschel ya gaya min cewa aikina na musamman a Bethel shi ne taimaka wa Ɗan’uwa Franz. Nakan karanta masa abubuwan da ake son a buga. Ɗan’uwa Franz yana riƙe abubuwa a kansa kuma yakan mai da hankali sosai a kan abin da ake karanta masa. Na yi farin cikin taimaka masa har ya gama hidimarsa a duniya a watan Disamba ta shekara ta 1992!

Gidan 124 Columbia Heights, inda na yi aiki shekaru da yawa

Shekaru 61 da na yi a Bethel kamar jiya ne. Iyayena sun mutu da amincinsu ga Jehobah, kuma ina jira in marabce su a sabuwar duniya. (Yoh. 5:​28, 29) Ba abin da za a iya gwada a duniyar nan da gatan yin hidima da maza da mata masu aminci don mutanen Allah a faɗin duniya su amfana. Ni da matata Livija mun ga cewa ‘Ubangiji shi ne ƙarfinmu’ a shekarun da muka yi hidima ta cikakken lokaci.​—Neh. 8:10.

Za a ci gaba da wa’azi a ƙungiyar Jehobah ko da me ya faru. Na yi farin ciki sosai da na yi aiki da ’yan’uwa da yawa masu ƙwazo da aminci shekaru da yawa. Yawancin ’yan’uwa shafaffu da na yi aiki da su ba sa duniya kuma. Amma na yi farin cikin zama abokin aiki da irin waɗannan mutane masu aminci a hidimar Jehobah.