Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 27

“Sa Zuciya ga Yahweh”

“Sa Zuciya ga Yahweh”

“Sa zuciya ga Yahweh, ka ƙarfafa, ka kasance da ƙarfin zuciya!”—ZAB. 27:14.

WAƘA TA 128 Mu Jimre Har Ƙarshe

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. (a) Waɗanne alkawura ne Jehobah ya yi mana? (b) Me ake nufi da “sa zuciya ga Yahweh”? (Ka duba “Ma’anar Wasu Kalmomi.”)

 JEHOBAH ya yi wa masu ƙaunarsa alkawarin abubuwa masu kyau a nan gaba. Ba da jimawa ba, zai kawar da rashin lafiya da baƙin ciki da mutuwa. (R. Yar. 21:3, 4) Zai taimaka wa “masu sauƙin kai” da suke dogara gare shi su maido da duniya ta zama aljanna. (Zab. 37:9-11) Kuma zai taimaka wa kowannen mu ya kasance da dangantaka mai kyau da shi fiye da yadda yake a yau. Hakan babban alkawari ne! Amma me ya tabbatar mana cewa Jehobah zai cika alkawuransa? Domin bai taɓa fasa cika alkawarinsa ba. Saboda haka, muna da dalili mai kyau na “sa zuciya ga Yahweh.” * (Zab. 27:14) Za mu nuna cewa muna hakan ta wajen yin haƙuri da kuma yin farin ciki yayin da muke jira Allahnmu ya cika alkawuransa.—Isha. 55:10, 11.

2. Mene ne Jehobah ya yi?

2 Jehobah ya riga ya nuna cewa yana cika alkawarinsa. Ga wani misali mai muhimmanci. A littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna, Jehobah ya yi alkawari cewa zai tattara mutane daga kowace al’umma da ƙabila da yare kuma zai sa su bauta masa cikin haɗin kai. A yau, waɗannan mutane na musamman su ne taro mai girma ko kuma “babban taro.” (R. Yar. 7:9, 10) Ko da yake rukunin ya ƙunshi maza da mata, manya da ƙanana da suka fito daga wurare dabam-dabam a duniya kuma suna yare dabam-dabam, dukansu ’yan’uwa ne kuma suna zama cikin haɗin kai. (Zab. 133:1; Yoh. 10:16) Suna kuma wa’azi da ƙwazo sosai. Suna a shirye a kullum su gaya wa mutane game da alkawura masu kyau da Allah ya yi mana. (Mat. 28:19, 20; R. Yar. 14:6, 7; 22:17) Idan kana cikin taro mai girman, babu shakka kana son alkawura da Jehobah ya yi sosai.

3. Mene ne burin Shaiɗan?

3 Iblis yana so ka daina sa zuciya a kan alkawuran Jehobah. Burinsa shi ne ya sa ka ɗauka cewa Jehobah bai damu da kai ba kuma ba zai cika alkawuransa ba. Idan Shaiɗan ya iya hana mu sa zuciya ga Jehobah, za mu iya sanyin gwiwa har mu daina bauta wa Jehobah gaba ɗaya. Kamar yadda za mu gani a gaba, Iblis ya yi ƙoƙari ya sa Ayuba ya daina sa zuciya ga Jehobah da kuma bauta masa.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin? (Ayu. 1:9-12)

4 A wannan talifin, za mu ga yadda Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya sa Ayuba ya daina bauta wa Jehobah. (Karanta Ayuba 1:9-12.) Za mu kuma tattauna abubuwan da za mu koya daga misalin Ayuba, da dalilin da ya sa ya kamata mu riƙa tuna cewa Allah yana ƙaunar mu kuma zai cika alkawuransa.

SHAIƊAN YA YI ƘOƘARIN SA AYUBA YA FID DA RAI

5-6. Me ya faru da Ayuba cikin ƙanƙanin lokaci?

5 Ayuba yana da dangantaka mai kyau da Jehobah, yana da babban iyali da ke da haɗin kai kuma shi mai arziki ne sosai. (Ayu. 1:1-5) Amma a rana ɗaya, ya yi hasarar kusan kome da yake da shi. Da farko, ya yi hasarar dukiyoyinsa. (Ayu. 1:13-17) Sai duka yaransa sun mutu. Ka yi tunanin irin wannan mummunan bala’i da ya faɗo masa. Ko da ma yaro ɗaya ne kawai ya mutu, iyaye suna baƙin ciki sosai. Balle a ce yara goma gaba ɗaya. Hakika, Ayuba da matarsa sun yi baƙin ciki sosai. Ba abin mamaki ba ne cewa Ayuba ya yage rigarsa, ya faɗi a ƙasa yana makoki!—Ayu. 1:18-20.

6 Bayan haka sai Shaiɗan ya bugi Ayuba da wani rashin lafiya da ya zubar masa da mutunci. (Ayu. 2:6-8; 7:5) Kafin lokacin, mutane suna daraja Ayuba sosai. Mutane sukan je wurinsa neman shawara. (Ayu. 29:7, 8, 21) Amma yanzu suna gudunsa. ’Yan’uwansa, da abokansa har ma da bayinsa sun yi banza da shi!—Ayu. 19:13, 14, 16.

A yau, ’yan’uwa maza da mata da yawa suna fuskantar irin jarrabobin da Ayuba ya fuskanta (Ka duba sakin layi na 7) *

7. (a) Wane ne Ayuba ya ɗauka cewa yana jawo masa bala’o’i, amma me ya ƙi yi? (b) Ta yaya Kirista zai iya fuskantar irin matsaloli da ke cikin hoton nan?

7 Shaiɗan ya so ya sa Ayuba ya ɗauka cewa Jehobah yana fushi da shi. Alal misali, wata guguwa mai ƙarfi ta hallaka gidan da ’ya’yan Ayuba guda goma suke liyafa a ciki. (Ayu. 1:18, 19) Ya kuma sa wuta ta fito daga sama ta hallaka dabbobin Ayuba tare da makiyayansu. (Ayu. 1:16) Da yake wuta da guguwar sun fito daga sama ne, Ayuba ya ɗauka cewa Jehobah ne ya turo su. A sakamakon haka, Ayuba ya yi tsammani cewa ya yi wani abu da ya ɓata wa Jehobah rai. Duk da haka, Ayuba ya ƙi ya la’anta Ubansa na sama. Ayuba ya yarda cewa Jehobah ya riga ya ba shi abubuwa masu kyau da yawa. Saboda haka, ya gaya wa kansa cewa, da yake ya ji daɗin alherin da Allah ya yi masa, bai kamata ya ƙi bala’in da Allah ya turo masa ba. Hakan ya sa shi ya ce: “Yabo ya tabbata ga Sunan Yahweh!” (Ayu. 1:20, 21; 2:10) Duk da cewa Ayuba ya yi hasarar dukiyoyinsa da yaransa kuma yana rashin lafiya, bai daina riƙe amincinsa ga Jehobah ba. Amma Shaiɗan bai bar shi ya huta ba.

8. Wace dabara ce kuma Shaiɗan ya yi amfani da ita?

8 A ƙarshe, Shaiɗan ya sake amfani da wata dabara dabam. Ya sa abokan Ayuba na ƙarya guda uku su sa shi ya ji kamar bai da amfani. Mutanen sun ce Ayuba yana shan wahala ne sakamakon zunubansa. (Ayu. 22:5-9) Ƙari ga haka, sun yi ƙoƙari su sa shi ya ji kamar ko da bai yi laifi ba, duk ƙoƙarinsa na bauta wa Jehobah banza ne. (Ayu. 4:18; 22:2, 3; 25:4) Za mu iya cewa sun yi ƙoƙari su sa Ayuba ya ji kamar Allah ba ya ƙaunarsa, cewa ba zai kula da shi ba kuma babu amfanin bauta wa Jehobah. Abin da suka faɗa zai iya sa Ayuba ya ji kamar ba shi da mafita.

9. Me ya taimaka wa Ayuba ya yi ƙarfin zuciya?

9 Ka yi tunanin abin da ke faruwa. Ga Ayuba yana zama a cikin toka, yana fama da zafin jiki. (Ayu. 2:8) Abokansa suna nan suna masa baƙar magana kuma suna ta cewa babu abin da ya taɓa yi da yake da amfani. Matsalolin da yake ciki, da baƙin ciki da yake yi don mutuwar yaransa sun fi gaban magana. Da farko, Ayuba bai ce uffan ba. (Ayu. 2:13–3:1) Idan abokansa suna gani kamar ya yi shiru don yana so ya bar Mahaliccinsa ne, to, sun yi kuskure. Da abin da suke faɗa ya ishe Ayuba, mai yiwu ya ɗaga kansa ya kalle su, sai ya ce musu: “Har in mutu ba zan daina riƙe amincina ba!” (Ayu. 27:5, New World Translation) Me ya taimaki Ayuba ya kasance da ƙarfin zuciya haka duk da wahalar da yake ciki? Ko a lokacin da yake baƙin ciki mai tsanani ma, bai fid da rai cewa Allahnsa mai ƙauna zai kawar da matsalolinsa ba. Ya san cewa ko da ya mutu, Jehobah zai tā da shi.—Ayu. 14:13-15, THS.

TA YAYA ZA MU YI KOYI DA AYUBA?

10. Mene ne muka koya daga labarin Ayuba?

10 Abin da muka koya daga labarin Ayuba shi ne, Shaiɗan ba zai iya tilasta mana mu daina bauta wa Jehobah ba, kuma Jehobah ya san kome da ke faruwa. Ƙari ga haka, labarin zai iya taimaka mana mu fahimci wasu batutuwa masu muhimmanci. Ka yi la’akari da wasu darussa kuma da za mu iya koya daga Ayuba.

11. Idan muka ci gaba da dogara ga Jehobah, wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi? (Yakub 4:7)

11 Ayuba ya nuna mana cewa idan muka ci gaba da dogara ga Jehobah, za mu iya jimre duk wata matsalar da za mu fuskanta kuma za mu iya yin tsayayya da Shaiɗan. Mene ne zai zama sakamakon hakan? Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan zai guje mu.—Karanta Yakub 4:7.

12. A wace hanya ce begen tashin matattu ya ƙarfafa Ayuba?

12 Muna bukatar mu ba da gaskiya sosai ga begen tashin matattu. A talifi na baya, mun koyi cewa Shaiɗan yana yawan yin amfani da tsoron mutuwa a ƙoƙarinsa na sa mu daina bauta wa Jehobah. Shaiɗan ya yi da’awa cewa Ayuba zai yi kome da zai iya yi, har ma ya daina bauta wa Jehobah, don ya ceci ransa. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Har a lokacin da Ayuba ya ɗauka cewa zai mutu ma, bai daina bauta wa Jehobah ba. Ya ba da gaskiya cewa Jehobah nagari ne, kuma begen da yake da shi ya taimaka masa ya jimre. Ayuba ya kuma ba da gaskiya cewa idan Jehobah bai taimaka masa sa’ad da yake da rai ba, Jehobah zai tā da shi daga mutuwa a nan gaba. Ayuba ya yarda da dukan zuciyarsa cewa za a tā da matattu. Idan mu ma mun ba da gaskiya ga tashin matattu, ko da an ce za a kashe mu, ba za mu daina bauta wa Jehobah ba.

13. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga dabarun da Shaiɗan ya yi amfani da su a kan Ayuba?

13 Wajibi ne mu mai da hankali sosai ga dabarun da Shaiɗan ya yi amfani da su yayin da yake ƙoƙarin rinjayar Ayuba, domin Shaiɗan yana amfani da su har wa yau. Ka lura da abin da Shaiɗan ya faɗa. Ya ce: ‘Mutum [ba Ayuba kaɗai ba] zai iya ba da dukan abin da yake da shi domin ya ceci ransa.’ (Ayu. 2:4, 5) Saboda haka, abin da Shaiɗan yake cewa shi ne, ba ma ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu kuma za mu daina bauta masa idan ranmu na cikin haɗari. Ƙari ga haka, Shaiɗan yana da’awar cewa Jehobah ba ya ƙaunar mu kuma ba ya damuwa da ƙoƙarin da muke yi mu faranta masa rai. Da yake mun san burin Shaiɗan, ba ma yarda da ƙaryar nan.

14. Mene ne matsaloli za su iya taimaka mana mu gano? Ka ba da misali.

14 Idan muna fuskantar gwaji, hakan zai iya ba mu damar bincika kanmu. Matsalolin da Ayuba ya fuskanta sun taimaka masa ya san inda ya kamata ya gyara halinsa. Alal misali, ya gane cewa yana bukatar ya daɗa kasancewa da sauƙin kai. (Ayu. 42:3) Mu ma za mu iya bincika kanmu sosai a lokacin da muke fuskantar matsaloli. Wani ɗan’uwa mai suna Nikolay, * da aka kai shi kurkuku duk da cewa yana rashin lafiya mai tsanani, ya ce: “Kamar yadda na’urar X-ray take taimaka wa likita ya ga cikin jikin ɗan Adam, haka ma yanayi mai wuya zai iya taimaka mana mu fahimci inda muke bukata mu gyara halinmu.” Da zarar mun san inda muke da kasawa, sai mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi gyara.

15. Wa ya kamata mu saurare shi, kuma me ya sa?

15 Muna bukatar mu saurari Jehobah, ba maƙiyanmu ba. Ayuba ya saurara da kyau yayin da Jehobah yake masa magana. Allah ya yi wa Ayuba wasu tambayoyi don ya taimake shi ya fahimci cewa Allah ya damu da shi sosai. Ayuba ya tuba kuma ya nuna sauƙin kai da godiya don alherin da Jehobah ya yi masa. Ya ce: “Dā na ji labarinka da kunne kawai, amma yanzu idanuna sun gan ka.” (Ayu. 42:5) Mai yiwuwa Ayuba yana zaune a cikin toka har ila, jikinsa cike da marurai kuma yana kan makokin yaransa sa’ad da ya furta kalmomin nan. Duk da haka, Jehobah ya nuna wa Ayuba cewa Yana ƙaunar shi sosai kuma ya amince da shi.—Ayu. 42:7, 8.

16. Bisa ga Ishaya 49:15, 16, me ya kamata mu riƙa tunawa idan muna fuskantar matsaloli?

16 A yau, mutane za su iya zagin mu kuma su ɗauke mu a matsayin marasa daraja. Za su iya yin ƙoƙari su ɓata sunanmu ko sunan ƙungiyar Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Da ƙarya kuma za su ambato ku da kowace irin mugunta.’ (Mat. 5:11, THS) Daga labarin Ayuba, mun ga cewa Jehobah ya tabbata cewa za mu riƙe amincinmu idan muna fuskantar matsaloli. Jehobah yana ƙaunar mu kuma ba zai taɓa yar da waɗanda suka dogara gare shi ba. (Karanta Ishaya 49:15, 16.) Kada ku mai da hankali ga ƙaryace-ƙaryace da maƙiyan Allah suke yaɗawa game da ku! Wani ɗan’uwa daga ƙasar Turkiyya mai suna James, wanda shi da iyalinsa sun fuskanci jarrabawa sosai, ya ce: “Mun fahimci cewa sauraron ƙaryace-ƙaryacen da ake yaɗawa game da mutanen Allah zai sa mu sanyin gwiwa. Saboda haka, mun mai da hankali ga abubuwa da Mulkin Allah zai yi mana a nan gaba, kuma mun ci gaba da ayyukan ibada. Hakan ya sa ba mu daina farin ciki ba.” Kamar yadda Ayuba ya yi, mu ma muna sauraron Jehobah. Ƙaryace-ƙaryacen da maƙiyanmu suke yaɗawa ba za su hana mu sa zuciya ba!

KASANCEWA DA BEGE ZAI TAIMAKE KA KA JIMRE

Jehobah ya yi wa Ayuba albarka don yadda ya jimre kuma ya ba shi da matarsa tsawon rayuwa (Ka duba sakin layi na 17) *

17. Me ka koya daga misalin maza da mata masu aminci da aka ambata a Ibraniyawa sura 11?

17 Ayuba ɗaya ne daga cikin bayin Jehobah da suka nuna ƙarfin zuciya kuma suka jimre jarrabawa mai tsanani. A littafin Ibraniyawa, manzo Bulus ya ambata mutane masu aminci da yawa kuma ya kira su “taron shaidu masu yawa ƙwarai.” (Ibran. 12:1) Dukan su sun fuskanci jarrabawa sosai. Duk da haka sun riƙe amincinsu ga Jehobah har mutuwarsu. (Ibran. 11:36-40) Shin, yadda suka jimre da kuma ayyukan da suka yi wa Jehobah sun zama banza ne? A’a! Ko da yake ba su ga cikar dukan annabce-annabcen da Jehobah ya yi ba, sun ci gaba da dogara ga Jehobah. Kuma da yake sun tabbata cewa suna da amincewar Jehobah, ba su yi shakka cewa za su ga cikar annabce-annabcen ba. (Ibran. 11:4, 5) Misalinsu zai iya taimaka mana mu ma mu dogara ga Jehobah.

18. Me ka ƙudura cewa za ka yi? (Ibraniyawa 11:6)

18 A yau, muna rayuwa a duniya da take daɗa muni. (2 Tim. 3:13) Shaiɗan bai gama jarraba bayin Allah ba tukuna. Bari mu ƙudura cewa za mu ci gaba da bauta wa Jehobah da dukan ƙarfinmu ko da wace matsala ce muka fuskanta a gaba. Kuma mu tabbatar wa kanmu cewa “mun sa zuciyarmu ga Allah Mai Rai.” (1 Tim. 4:10) Ka tuna cewa sakamakon da Ayuba ya samu don jimirinsa ya nuna cewa “Ubangiji mai jinƙai ne, mai yawan tausayi kuma.” (Yak. 5:11) Bari mu ma mu riƙe amincinmu ga Jehobah kuma mu tuna cewa zai “ba da lada ga duk waɗanda suke nemansa.”—Karanta Ibraniyawa 11:6.

WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto

^ Idan aka yi maganar mutumin da ya fuskanci gwaji mai tsanani, za mu iya tunanin Ayuba. Me za mu iya koya daga labarin wannan mutum mai aminci? Mun ga cewa Shaiɗan ba zai iya tilasta mana mu bar Jehobah ba. Mun kuma ga cewa Jehobah ya san kome da kome da ke faruwa da mu. Kuma kamar yadda Jehobah ya kawo ƙarshen gwajin da Ayuba ya fuskanta, mu ma Jehobah zai kawar da wahalar da muke sha wata rana. Idan halinmu ya nuna cewa mun yarda da hakan, za mu nuna cewa muna “sa zuciya ga Yahweh.”

^ MA’ANAR WASU KALMOMI: Kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “sa zuciya” tana iya nufin yarda da mutum ko kuma dogara gare shi.—Zab. 25:2, 3; 62:5, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

^ An canja wasu sunayen.

^ BAYANI A KAN HOTUNA: Ayuba da matarsa a lokacin da dukan yaransu suka mutu.

^ BAYANI A KAN HOTUNA: Ayuba ya jimre jarrabawa har ƙarshe. Shi da matarsa suna tunanin albarka da Jehobah ya yi wa iyalinsu.