HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Janairu 2018

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 26 ga Fabrairu–1 ga Afrilu, 2018.

SUN BA DA KANSU DA YARDAR RAI

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Madagaska

Ka karanta labarin wasu ʼyan’uwa maza da mata da suka kaura zuwa kasar Madagaska don yin wa’azi game da Mulkin Allah a kasar gabaki daya.

‘Yana Ba da Karfi ga Masu Kasala’

Yayin da karshen wannan zamanin yake kusatowa sosai, mun san cewa matsaloli za su dada karuwa. Jigonmu na 2018 ya tuna mana cewa mu rika dogara ga Jehobah.

Taron Tuna da Mutuwar Yesu na Kawo Hadin Kai

A wadanne hanyoyi ne taron Tuna da Mutuwar Yesu yake sa mutanen Allah su kasance hadin kai? Yaushe ne za a yi taron Tuna da Mutuwar Yesu na karshe?

Me Za Mu Iya Ba Wanda Yake da Kome?

Wata hanya da muke nuna cewa muna kaunar Allah ita ce ta ba da gudummawa. Ta yaya muke amfana ta daraja Jehobah da dukiyarmu?

Nuna Wace Irin Kauna Ce Ke Sa Mu Farin Ciki?

Ta yaya kaunar Allah ta yi dabam da kaunar da aka ambata a 2 Timotawus 3:​2-4? Amsoshin za su taimaka mana mu samu gamsuwa da farin ciki.

Za Ku Ga Bambancin da Ke Tsakanin Mutane

Wane bambanci ne ke tsakanin halayen da yawancin mutane za su kasance da shi a kwanaki na karshe da kuma na bayin Allah?

Ka Sani?

A zamanin dā, ana amfani da dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa don a sasanta dukan matsaloli?