Koma ka ga abin da ke ciki

GANAWA | RACQUEL HALL

Wata Bayahudiya Ta Bayyana Abin da Ya Sa Ta Sake Bincika Imaninta

Wata Bayahudiya Ta Bayyana Abin da Ya Sa Ta Sake Bincika Imaninta

Mahaifiyar Racquel Hall ’yar Isra’ila ce, mahaifinta kuma mutumin Austria ne da ya shiga addinin Yahudawa. Iyayen mahaifiyarta masu gwagwarmayar neman ’yancin Yahudawa ne da suka koma kasar Isra’ila a 1948, shekarar da kasar ta sami ’yanci. An tattauna da Racquel wadda ita ma mabiyar addinin Yahudawa ce kuma ta fadi abin da ya sa ta sake bincika imaninta da kyau. An rubuta hirar da aka yi da ita a mujallar Awake!

Ki dan ba mu tarihinki.

An haife ni a kasar Amirka a 1979. Ina ’yar shekara uku, sai iyayena suka raba aurensu. Mamata ta koya min al’adun Yahudawa kuma ta kai ni makarantun Yahudawa da ake kira yeshiva. Da na kai shekara bakwai, mun kaura zuwa kasar Isra’ila kuma mun yi shekara daya a wurin. A can na rika zuwa makaranta a wani unguwa da ma’aikata suke zama, ana kiransa kibbutz. Daga baya ni da mahaifiyata muka kaura zuwa Meziko.

Ko da yake babu majami’ar Yahudawa a wurin, na ci gaba da bin al’adun Yahudawa. Nakan kunna kyandir don Ranar Assabaci, in karanta Attaura, kuma ina amfani da littafin addu’a da ake kira siddur wajen yin addu’a. A makaranta, nakan gaya wa ’yan ajinmu cewa addininmu ne ainihin addini na gaskiya. Ban taba karanta littattafan da ake kira Sabon Alkawari ba, kuma su ne suka yi bayani sosai a kan hidimar Yesu da koyarwarsa. Mahaifiyata ta ja min kunne cewa kada in karanta su don kada su bata imanina.

Me ya sa kika yanke shawarar karanta Sabon Alkawari?

Da na kai shekara 17, na kaura zuwa Amirka don in kammala karatuna. A Amirka, wani Kirista da na saba da shi ya ce min idan har ban yi imani da Yesu ba, to, da sauran labari ke nan.

Sai na ce masa: “Wadanda suka yi imani da Yesu suna cikin duhu.”

Sai ya tambaye ni: “Kin taba karanta Sabon Alkawari?”

Na ce masa “a’a.”

Sai ya ce min, “Wannan da kike fadin ra’ayinki a kan abin da ba ki san kome a kai ba, anya, ba rashin sani ne yake damun ki ba?”

Abin da ya fada ya ratsa zuciyata, don na san cewa wawanci ne mutum ya kama fadin ra’ayinsa a kan abin da bai sani ba. Don haka, na karbi Littafi Mai Tsarki daga wurinsa, na je gida kuma na soma karanta Sabon Alkawari.

Yaya abin da kika karanta ya shafe ki?

Na yi mamaki da na ga cewa wadanda suka rubuta Sabon Alkawari Yahudawa ne. Yayin da nake karatun, na ga cewa Yesu Bayahuden kirki ne, kuma mai tawali’u ne da ya yi kokarin taimaka wa mutane, ba cutar da su ba. Har na je laburare na ari littattafai game da Yesu. Amma littattafan ba su sa na yarda cewa Yesu ne Almasihu ba. Wasunsu ma sun ce Yesu shi ne Allah, abin da na san karara cewa ba haka ba ne. Da Yesu ya yi addu’a, ga wa ya yi addu’ar? Ban da haka, Yesu ya mutu. Amma Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da Allah cewa: “Ba ka mutuwa!” *

Ya kika yi kika san gaskiyar?

Na san cewa gaskiya daya ce, don haka na kudura cewa sai na san gaskiyar. Na yi addu’a ga Allah da dukan zuciyata, har da kuka. Wannan shi ne karo na farko da na yi addu’a ba tare da yin amfani da littafin addu’armu ba. Bayan na gama addu’ar, sai na ji an kwankwasa kofata. Shaidun Jehobah ne guda biyu. Sun ba ni wata kasida da suke amfani da ita don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Kasidar nan da abubuwan da na koya daga tattaunawa da muka yi ta yi da su ya tabbatar min cewa koyarwarsu daga Littafi Mai Tsarki ne. Alal misali, Shaidun Jehobah sun yi imani cewa Yesu ba daya yake da Allah ba. Maimakon haka, sun yi imani cewa shi “Ɗan Allah ne,” * da kuma “farkon halittar Allah.” *

Ba da dadewa ba bayan haka, na koma Meziko, kuma na ci gaba da nazarin annabce-annabce da aka yi game da Almasihu tare da Shaidun Jehobah. Yawan annabce-annabcen ya ba ni mamaki! Duk da haka, ban daina yin shakka ba. Na ce: ‘Anya Yesu ne kadai ya cika duka annabce-annabcen nan? Idan shi wani mai wayo ne da ya yi kamar shi ne Almasihu fa?’

Me ya sa kika daina shakka?

Shaidun Jehobah sun nuna min annabce-annabcen da babu wani mayaudarin da zai iya cika su. Alal misali, fiye da shekara 700 kafin a haifi Almasihu, annabi Mika ya annabta cewa a Bai’talami na Yahudiya ne za a haife shi. * Akwai wanda zai iya zaban inda za a haife shi? Annabi Ishaya ya annabta cewa za a kashe Almasihu a matsayin mai aikata laifi, amma za a binne shi a wurin da ake binne masu arziki. * Yesu ya cika duka annabce-annabcen nan.

Tabbaci na karshe da na samu game da zuriyar da Yesu ya fito ne. Littafi Mai Tsarki ya ce Almasihu zai fito daga zuriyar Sarki Dauda. * Yahudawa a dā sukan ajiye bayanai game da zuriyarsu. Da a ce Yesu bai fito daga zuriyar Dauda ba, da makiyansa sun yi ta fadan hakan a fili don su karyata shi. Amma ba su yi hakan ba, domin babu shakka cewa Yesu ya fito daga zuriyar Dauda ne. Jama’a ma sun yi ta kiransa ‘Dan Dauda!’ *

A shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu, wato shekaru 37 bayan mutuwar Yesu, sojojin Roma sun hallaka Urushalima kuma bayanai game da zuriyar mutanen Isra’ila sun bata ko kuma an hallaka su. Don haka, dole ne Almasihu ya bayyana kafin shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu. In ba haka ba, ba yadda za a tabbatar da zuriyar da ya fito.

Me kika yi da kika fahimci hakan?

A littafin Maimaitawar Shari’a 18:​18, 19, an annabta cewa Allah zai aiko wani annabi a Isra’ila kamar Musa. Allah ya ce: “Duk wanda bai kasa kunne ga kalmomin da annabin nan zai faɗa a cikin Sunana ba, ni da kaina zan nemi alhakin kalmomin daga wannan mutumin.” Yin nazarin Littafi Mai Tsarki gabaki dayansa da kyau ya tabbatar min cewa Yesu Banazare ne wannan annabin.

^ sakin layi na 15 Habakkuk 1:​12.

^ sakin layi na 17 Yohanna 1:34.

^ sakin layi na 17 Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 3:​14, Tsohuwar Hausa a Saukake.

^ sakin layi na 20 Mika 5:2; Matiyu 2:1.

^ sakin layi na 20 Ishaya 53:​3, 7, 9; Markus 15:​43, 46.

^ sakin layi na 21 Ishaya 9:​6, 7; Luka 1:​30-32. A Matiyu sura 1, an rubuta zuriyar da Yusufu mijin Maryamu ya fito, a Luka sura 3 kuma, an rubuta zuriyar da mahaifiyar Yesu Almasihu ta fito.

^ sakin layi na 21 Matiyu 21:9.