Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Nemi Sanin Raꞌayin Allah

Ku Nemi Sanin Raꞌayin Allah

Ya kamata mu riƙa faranta ran Jehobah a duk abubuwan da muke yi. (K. Ma 27:11) Don mu yi haka, muna bukata mu tsai da shawarwarin da suka jitu da raꞌayin Allah, ko da babu wata takamaiman dokar da za mu bi. Amma me zai taimaka mana?

Zai dace mu riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki. A duk lokacin da muka karanta Littafi Mai Tsarki, kamar muna sauraron Jehobah ne. Za mu iya sanin raꞌayin Jehobah ta wajen lura da yadda ya yi shaꞌani da mutanensa da kuma bincika misalan waɗanda suka yi abin da ya dace da waɗanda ba su yi abin da ya dace ba a gabansa. Idan muna so mu yanke shawara, ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu tuna da muhimman darussa da ƙaꞌidodin da muka koya daga Kalmar Allah.​—Yoh 14:26.

Ku riƙa bincike. Idan kana so ka yanke shawara, ka tambayi kanka, ‘waɗanne ayoyi ne ko labarai a Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mini in san raꞌayin Jehobah a kan wannan batun?’ Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka kuma ka yi amfani da kayan binciken da ke yarenku don ka sami ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka maka a yanayinka, kuma ka yi amfani da su.​—Za 25:4.

KU KALLI BIDIYON NAN WAJIBI NE KU YI TSERE DA JIMIRI​—KU CI ABINCI MAI GINA JIKI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne matashiyar da aka nuna a bidiyon ta fuskanta?

  • Ta yaya za ka yi amfani da kayan bincike saꞌad da ka fuskanci irin matsalolin nan?

  • Ta yaya za mu amfana idan muka yi bincike kuma muka yi nazarin da zai taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau?​—Ibr 5:​13, 14