Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Kana Fahimtar Halayen Allah Kuwa?

Kana Fahimtar Halayen Allah Kuwa?

Shin kana ganin ɗaukakar mahaliccinmu idan ka ga fure mai kyau da taurari da kuma walƙiya in ana ruwan sama? Halittu da ke kewaye da mu suna nuna mana halaye masu kyau na Jehobah da ba ma iya gani. (Ro 1:20) Idan mun dakata mun yi tunani a kan abubuwa da muke gani da idanunmu, za mu fahimci ikon Allah da ƙaunarsa da adalcinsa da kuma alherinsa.​—Za 104:24.

Waɗanne halittun Jehobah ne kake gani a koyaushe? Ko da a birni kake zama, za ka iya ganin tsuntsaye ko kuma itatuwa. Yin tunani a kan halittun Jehobah, zai taimaka mana mu rage yawan damuwa. Zai sa mu mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci idan muna cikin damuwa kuma zai sa mu ƙara dogara ga Jehobah cewa zai ci gaba da biya mana bukatunmu har abada. (Mt 6:​25-32) Idan kana da yara, ka taimaka musu su fahimci halayen Jehobah masu kyau. Yayin da muke ci gaba da yin tunani a kan halittun Jehobah, za mu ƙara kusantar Mahaliccinmu.​—Za 8:​3, 4.

KU KALLI BIDIYON NAN HALITTU SUNA NUNA ƊAUKAKAR ALLAH​—HASKE DA KALA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne yake sa mu iya ganin kala?

  • Me ya sa wasu kala da ke jikin dabbobi sukan canja idan dabbar ta juya?

  • Me ya sa muke ganin kaloli dabam-dabam a sama?

  • Waɗanne kaloli masu ban sha’awa ne kuma kake gani a kusa da gidanka?

  • Me ya sa ya dace mu riƙa tunani a kan halittun Jehobah?

Mene ne haske da kala suka koya mana game da halayen Jehobah?