Koma ka ga abin da ke ciki

14 GA FABRAIRU, 2017
AMIRKA

Wata Kungiya da Ake Kira GBI Ta Yaba Wa Shaidun Jehobah Don Ingantaccen Sabon Ginin Hedkwatarsu

Wata Kungiya da Ake Kira GBI Ta Yaba Wa Shaidun Jehobah Don Ingantaccen Sabon Ginin Hedkwatarsu

NEW YORK​—⁠An yaba wa Shaidun Jehobah bayan sun kammala ingantacen ginin sabon hedkwatarsu a garin Warwick da ke jihar New York a Agusta 2016. Green Building Initiative (GBI), kungiya ce wadda take kula da harkar gyara mahalli da kuma tabbatar da cewa gine-ginen da ake yi don kasuwanci suna bisa ka’ida, kungiyar ta ba Shaidun Jehobah lambar yabo na musamman na Four Green Globes ma duka gine-ginensu bakwai da suka cancanci a ba su.

Wata babban darekta na GBI mai suna Shaina Weinstein, ta ce: “A duka gine-gine 965 a fadin kasar, gini 64 ne suka samu yabo na musamman na Four Green Globes. Babban abu ne yadda Shaidun Jehobah suka samu yabo na Four Green Globes don duka gine-ginensu bakwai na Warwick. An cim ma hakan ne domin sun bi ka’idodin da aka tsara game da ruwa da na lantarki da kuma kulawa da mahalli.”

Yadda Green Globes suke tsara kyaun gini, shiri na GBI. Duk gine-gine bakwai na hedkwatar Shaidun Jehobah da aka amince da su sun sami lambar yabo da ya kai kashi 90 bisa 100, kuma ya yi daidai da Four Green Globes.

A dandali Kungiyar GBI na intane, an bayyana cewa, “kungiya GBI, kungiya ce wadda ba ta kasuwanci amma ta na mai da hankali ga yadda za a yi gini ba tare da bata kudi da yawa ba, kuma a sami lafiyayar mahalli mai inganci. Kungiyar GBI ta na ba da tsari game da yadda za a yi gini mai sauki da kuma yadda za a kiyaye sabbin gine-gine. Cikin tsari aikinsu, wani kwararre daga zai bincika filin ya tabbatar da abin da GBI ta gani.

Wani mai suna David Bean, wanda shi ne mai kula da zane-zane na ginin Shaidun Jehobah a Amirka, ya ce: “Muna godiya da wadannan lambar yabo da aka ba mu, wannan ya nuna cewa mutanen da suka taimaka don yin wannan aikin gini sun yi hakan da zuciya daya. Kari ga haka, ya nuna yadda ingantaccen gini ya kamata ya kasance. Kuma ginin yana bisa ka’ida da sauran gine-ginen da ke Lambun Sterling Forest State.”

Ginin Ofisoshi da Wuraren Hidimomi masu rufin ganye da fure da ke girma a bisansu. An tsara yadda ruwan da ke zuba daga rufin ba zai yi wani lahani ga ruwan da mutane suke sha a birnin.

Shaidun sun bar wasu bishiyoyi da ke filin kuma sun yi amfani da wadanda suka sare wajen yin ginin. Manajan Starlin Forest na dā mai suna Jeffrey Hutchinson ya ce, “Na ji dadin shawarar yin amfani da itatuwan da aka sare domin a samu wurin gini kuma a yi amfani da su wajen yin sabuwar ginin.” Shaina Weinstein ta ce: “Abin da Shaidun Jehobah suka yi game da mahallin ya yi kyau sosai. A ra’ayinmu, ginin Warwick ya nuna abin da ya kamata masu gine-gine su yi la’akari da shi yayin da suke zanen gini, wato kyaun mahallin.”

Wani mai suna Richard Devine wanda shi ne mai kujerar kwamitin ginin Shaidun Jehobah na Warwick ya ce: “Shekaru da dama, kungiyarmu ta adana kyaun gininmu na Brooklyn. A yanzu dai za mu ci gaba da kiyaye gininmu na Warwick da kuma inganta kyaun lambun Sterlin Forest.”

Inda Aka samo Labarin:

David  A. Semonian, Office of Public Information, 1-845-524-3000

 

Fadin filin hedkwatar Shaidun Jehobah da ke Warwick, New York, yana kasa da kashi 20 bisa 100 na eka 253 da aka tsaya a 17 ga Yuli, 2009.

An jera duwatsu manya da kanana kewaye da ginin saboda ya kare ginin.

Manyan duwatsun da aka haka a filin lokacin da aka fara ginin. Nauyin duwatsun da aka haka kuma aka sake amfani da su sun kai tan 240,000.

Domin a kare tafkin Blue Lake daga yin ambaliya, an saka wata na’ura a gefen tafki domin wannan.

Wurin zub da lalataccen abubuwan da za a sake amfani da su. An kwashe tarkacen wurin gini sama da kashi 70 bisa 100 zuwa wurin da ake iya juyawa don amfani da su.

Ma’aikata suna shuka fure kusa da kofar shigar hedkwatar Shaidun Jehobah. An yi adon mahallin da itatuwa da shuke-shuke da kuma ciyayin rufe kasa kamar taburma.

Ma’aikata suna saka na’urar kawo dumi wanda ke nitsewa har zurfin kafa 499. Awon yanayin na cikin kasa ya yi daidai. Na awon yanayin na sarari kuma yana canja a lokacin rani da na sanyi. Na’urar da ke sauya yanayin sanyi tana amfani da zafin da ke cikin kasa, sai ya jawo zafin kasa domin taimaka wa ginin ya yi dumi a lokacin sanyi, lokacin rani kuma sai na’urar ya rage zafin daga ginin. Wannan na’urar da Shaidun Jehobah suka saka zai rage yawan wutan lantarki da za a yi amfani da shi don kawo dumi ko sanyi ga gine-ginen zuwa kashi 40 bisa 100.

Ginin Ofisoshi da Wuraren Hidimomi. Aikin da aka yi a cikin ginin (Kamar su fanti da bango da kuma saka silin) duk sun bi ka’idar kungiyar Green Building Initiative ta wurin yin amfani da (abubuwan da ba sa kawo cuta), kuma hakan yana kare lafiyar masu zama a wurin.