SASHE NA 13
Mene Ne Muke Bukatar Mu Yi Don Mu Faranta wa Allah Rai?
Ka guje wa abin da ba shi da kyau. 1 Korintiyawa 6:9, 10
Idan muna ƙaunar Jehobah, ba za mu yi abubuwan da ba ya so ba.
Jehobah ba ya son mu yi sata, maye, ko mu sha ƙwayoyi masu bugarwa.
Allah ya ƙi jinin yin kisa, zubar da ciki, da luwaɗi. Ba ya son mu kasance masu haɗama ko mu yi faɗa da mutane.
Kada mu bauta wa gumaka ko mu yi sihiri.
Ba za a ƙyale mutanen da ke yin mugun abubuwa su shiga Aljanna mai zuwa a duniya ba.
Ka yi abin da yake da kyau. Matta 7:12
Don mu riƙa faranta wa Allah rai, dole ne mu yi koyi da shi.
Ka nuna ƙauna ga mutane ta wajen yi musu alheri da karimci.
Ka kasance mai gaskiya.
Ka kasance mai nuna tausayi da gafartawa.
Ka gaya wa mutane game da Jehobah da hanyoyinsa.—Ishaya 43:10.

