Dakin Watsa Labarai
Hukumomin Rasha Suna Kokarin Rufe Ofishin Shaidun Jehobah
Wata wasikar gargadi da aka tura wa Shaidun Jehobah ya nuna cewa hukumomin Rasha suna kokarin dakatar da ayyukansu na ibada da kuma na koya wa mutane Littafi Mai Tsarki a Rasha.
Sashen Tunawa da Kisan Yahudawa da ke Kasar Hungary Ya Bude Hoton Dutse don Girmama Shaidun da Hitila Ya Yi wa Kisan Kiyashi
A Sashen Tunawa da Kisan Yahudawa a Budapest, an bude hoton dutse na Shaidun Jehobah guda hudu da hitila ya yi musu kisan kiyashi a lokacin Yakin Duniya na Biyu don sun ki shiga aikin soja.
An Kai Musu Hari Domin Imaninsu a Gabashin Ukraine
Mutane dauke da makamai sun saci Shaidun Jehobah guda 26 kuma sun gana musu azaba domin su ba ’yan addinin Orthodox ba ne kuma ba ruwansu da siyasa. Shaidun sun ki su musanta imaninsu.
Kotun Ruwanda Ya Amince da Kasancewar Addinai Dabam-dabam
Wani Kotu a yankin Karongi a Ruwanda ya goyi bayan ’yancin addini wa dalibai takwas da Shaidun Jehobah ne. Shawarar da kotun ya yanke zai iya taimaka a amince da kasancewar addinai dabam dabam a makarantu na kasar Ruwanda kuwa?
Babban Kotun Isra’ila Ya Daukaka ’Yancin Shaidun Jehobah na Yin Babban Taro Cikin Salama
Hukumomin Isra’ila sun yi tir da wariyar addini ta wajen kāre ’yancin Shaidun Jehobah na yin taro don ibada.
Shaidu Sun Yi Kira da A Saki Matan da Aka Tsare a Azerbaijani
Ana tsananta wa Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova kamar yadda ake yi wa masu laifi mai tsanani domin sun yi magana da wasu game da imaninsu. Shin, Azerbaijani za ta nuna cewa tana daukaka ’yancin addini kamar yadda take da’awa?
Shaidun Jehobah Sun Yi Kira da A Daina Tsare ’Yan’uwansu Ba Bisa Ka’ida Ba a Azerbaijani
Shin Azerbaijani za ta ba kowa ’yancin bin addini kamar yadda take da’awa ta wurin sake wadannan mata biyu, wato Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova, kuma ta bar Shaidun Jehobah su yi ibadarsu cikin salama?