Dakin Watsa Labarai
Kotun Kazakhstan Ta Jefa Wani Mashaidin Jehobah Marar Lafiya Kurkuku Kuma Ta Hana Shi Yin Ibadarsa
An yanke wa Teymur Akhmedov, mai mata da kuma yara maza uku,hukuncin shekara biyar a kurkuku don yana ayyukan addininsa.
Shaidun Jehobah Sun Sayar da Wani Ginin da Ke Hedkwatarsu na Dā
Shaidun Jehobah da ke aiki a hedkwatarsu sun yi shekara fiye da 50 suna zama a cikin ginin.
Shaidun Jehobah Sun Soma Taron Yanki
Shaidun Jehobah suna gayyatar mutane zuwa taron yanki na kwana uku mai jigo “Kar Ka Gaji!” da za a soma daga ranar 19 ga Mayu, 2017.
An Kusan Kammala Rarraba Kayan Agaji don Guguwar Matthew a Haiti
Ana so a kammala wannan aiki a watan Yuni 2017.
Kasar Kazakhstan Ta Hana Teymur Akhmedov Yin Ayyukan Ibada Kuma An Jefa Shi a Kurkuku
Duk da cewa Malam Akhmedov ba shi da isasshen lafiya, wata kotu a Astana ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyar a kurkuku don yana wa’azi.
Ruwan Sama Ya Yi Bala’in Barna a Ajantina
Babu wani cikin Shaidun Jehobah da ya rasa ransa ko ya ji wani rauni a wannan bala’in da ya afko a jihohi 13 a Ajantina.
Shaidun Jehobah Sun Dauki Matakin Gyara Gidaje Bayan Wata Mahaukaciyar Guguwar Super Typhoon Nock-Ten Ta Yi Barna
Shaidun Jehobah suna taimaka wa wajen gyaragidaje da yawa bayan bala’in ta auku a Filifin a karshen 2016.
Shaidun Jehobah Sun Taimaka Wajen Gyaran Gidaje 300 Da Girgizar Kasa Ta Lalata a Japan
Masu aikin gine-gine na Shaidu sun kammala wata gaggarumar aiki, gyaran gidajen ‘yan’uwansu.
Kotun Kolin Rasha Ta Hana Shaidun Jehobah Yin Ayyukan Ibadarsu
Shaidun Jehobah za su sake daukaka hukuncin da aka yanke na rufe Ofishinsu a kasar Rasha.
Rana Ta Biyar Da Kotun Koli Ta Rasha Ke Shari’a: An Sake Bincike Kalubalen Da Shaidun Jehobah Suka Fuskanta Cikin Shekara Goma Da Suka Shige
Lauyoyin Hukumar Shari’a ta Rasha ba su iya ba da kwakwarar dalilin da ya sa za a yi fakon Ofishin Shaidun Jehobah ba.
Kotun Kolin Rasha Ya Sake Sauraron Kara A Rana Ta Hudu
Lauyoyin ba su da kwakkwarar hujja da za su sa a rufe Ofishin Shaidun Jehobah a Rasha.
Shaidun Jehobah Sun Ba da Nasu Shaidar a Rana ta Uku na Sauraron Shari’a a Kotun Kolin Rasha
Shaidun Jehobah hudu sun ba da shaidar da ta nuna cewa zargin da Ma’aikatar Shari’a take yi wa Shaidun Jehobah cewa su masu tsattsauran ra’ayi ne kuma suna rarraba littattafai masu koyar da tsattsauran ra’ayi bai dace ba.

