Labarin Hidimar Yesu
Ka kalli wannan bidiyo mai dadi don ka koya game da Yesu Kristi Dan Allah wanda ya ceci mutane.
Sashe na 1: Hasken Gaske a Duniya
Ta yaya za a ceci mutane daga zunubin da suka gada daga Adamu? Almasihu ne kawai zai magance matsalar.
Sashe na 2: “Wannan shi Ne Ɗana”
Yohanna Mai Baftisma ne ya shirya wa Almasihu hanya. Ka lura da abubuwa masu ban mamaki da suka nuna lokacin da Yesu ya soma hidimarsa a duniya!
Sashe na Uku: “Ni Ne Shi”
Yesu ya gaya wa Nikodemus da mace Basamariya da kuma ꞌyan Nazaret cewa shi ne Almasihu, amma mutane kadan ne suka yarda da shi. Bayan da ya yi wata muꞌujiza, sai ya gaya ma wasu ꞌyan kamun kifi cewa su bi shi.
Sashe na 4: “Dalilin da Ya Sa Na Zo Ke Nan”
Yesu ya nuna cewa yana da iko ta wajen warkar da mutane da kuma fitar da aljannu. Amma wasu sun tsananta masa kuma suka kulla su kashe shi. Yesu ya iya yin waꞌazi da kuma zaɓan manzanninsa 12 don ya nuna tausayi sosai kuma ya iya koyarwa.
Sashe na 5: “Sai Jamaꞌar Suka Yi Mamaki Sosai don Yadda Yake Koyarwa”
Bayan Yesu wakar da mutane, ya soma koyar da su a hanyar da babu wani cikin malamansu da ya taɓa yin hakan. Ikon da yake da shi da kwatance-kwatancen da ya yi da kuma darussa masu amfani da ya koyar sun sa mutane mamaki.
Sashe na 6: “Kai ne Wanda Zai Zo?”
Yesu ya bayyana ikon da yake da shi na ta da matattu. Muꞌujizan da Yesu ya yi da koyarwarsa sun bayyana manufofin waɗanda suka saurare shi. Yesu ya yi amfani da misalai wajen bayyana wasu abubuwa game da Mulkin Allah.

