Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya

Wannan littafin zai taimaka maka ka ƙara kasancewa da bangaskiya da kuma ƙarfin zuciya.

Wasiƙa Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu tana fata cewa wannan littafin zai taimaka maka ka yi koyi da ƙarfin zuciya da maza da mata suka nuna a dā.

GABATARWA

Za Ka Iya Zama Mai Ƙarfin Zuciya Sosai!

Wannan littafin zai taimaka mana mu ƙara zama da ƙarfin zuciya. Ka lura da yadda Jehobah ya taimaka wa mutane ajizai su kasance da ƙarfin zuciyar da suke bukata, da kuma yadda zai taimaka maka.

SASHE NA 1

SASHE NA 1

Daga Lokacin Anuhu Zuwa Lokacin Samaꞌila

Wannan sashen na ɗauke da labarin mutane da suka nuna bangaskiya da ƙarfin zuciya. Daga Anuhu zuwa annabi Samaꞌila.

Sashe na 1 Lokacin da abubuwan suka faru

Hoton da ke nuna lokacin da wasu bayin Allah a Littafi Mai Tsarki suka rayu, da kuma wasu muhimman labaran Littafi Mai Tsarki.

1 ANUHU

Ya Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya

Anuhu ya fita dabam da mutane a zamaninsa a aƙalla a hanyoyi biyu. Ta yaya hakan ya yiwu? Mene ne muka koya game da ƙarfin zuciya daga wurinsa?

2 NUHU

Ta Bangaskiya Ya Tabbatar wa Duniya Laifinta

A waɗanne hanyoyi ne zamaninmu ya yi kama da zamanin Nuhu? Ka ga yadda za ka iya yin koyi da irin ƙarfin zuciya da Nuhu yake da shi.

3 SARATU

Ba Ta Yi Tunanin Komawa Ba

A waɗanne hanyoyi ne Saratu ta nuna bangaskiya da ƙarfin zuciya?

4 IBRAHIM

Mutum na Farko da Ya Yi Yaƙin da Jehobah Ya Amince

Mene ne muka koya daga yadda Ibrahim ya yi iya ƙoƙarinsa don ya ceci Lutu da iyalinsa? Mene ne Jehobah ya yi don ƙarfin zuciya da bangaskiya da ya nuna?

5 IBRAHIM

Abu Mafi Wuya da Ya Yi

Ta yaya za mu yi koyi da yadda Ibrahim ya nuna ƙarfin zuciya kuma ya yi wa Allah biyayya? Mene ne wannan labarin ya koya mana game da yadda ya kamata mu ƙaunaci Jehobah?

6 RIFKATU

Ta Bar Iyalinta Ta Je Inda Ba Ta Sani Ba

Rifkatu mace ce mai ƙarfin zuciya da bangaskiya sosai. Mene ne za mu iya koya daga misalinta?

7 YAKUBU

Ya Kāre Iyalinsa da Ƙarfin Zuciya

Ta yaya labarin Yakubu ya tabbatar maka cewa yana da kyau mu yi iya ƙoƙarinmu don mu sami albarkar Jehobah?

8 YUSUFU

Ya Guji Faɗawa Cikin Jaraba

Ka ga yadda misalin Yusufu zai taimaka maka ka guje wa jaraba, da kuma jimre matsaloli.

9 SHIFRA, FUWA, AMRAM, JOCHEBED DA MARYAMU

Ta Wurin Bangaskiya Ne Aka Ɓoye Musa

Mata masu karɓan haihuwa, da iyayen Musa, da kuma ꞌyarꞌuwarsa sun nuna ƙarfin zuciya da kuma bangaskiya sosai. Ta yaya mu ma za mu yi hakan?

10 MUSA

Ya Zaɓi Abin da Ya Fi Kyau

Wane zaɓi ne Musa ya yi, kuma me ya sa? Mene ne ka koya daga misalinsa?

11 MUSA

Ka Je Wurin Firꞌauna

Ta yaya labarin Musa ya tabbatar mana cewa Jehobah zai taimaka mana mu cika duk aikin da Ya ba mu ko da muna ganin ba za mu iya ba?

12 KALEB

Ya Kasance da Aminci ga Allah

Ka ga yadda labarin Kaleb zai taimaka mana mu guji “bin raꞌayin mutane da yawa.”

13 JOSHUWA

Ya Bi Umurnan da Allah Ya Ba Shi

Waɗanne umurnai ne Jehobah ya ba Joshuwa, kuma a waɗanne yanayoyi ne za mu iya yin koyi da misalin Joshuwa?

14 RAHAB

Ta Zaɓi Jehobah Maimakon Mutanenta

Me za mu iya koya daga abin da Rahab ta yi? Ta yaya Allah ya albarkace ta don bangaskiya da ƙarfin zuciya da ta nuna?

15 NAOMI DA RUT

Sun Taimaki Juna a Lokacin Wahala

A waɗanne hanyoyi ne Naomi da Rut suka nuna ƙarfin zuciya? Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga labarinsu?

16 BARAK DA DEBORA

“Hakika, Zan Tafi Tare da Kai”

Barak ya nace Debora ta bi shi zuwa bakin daga. Wannan alamar ragonci ne, ko kuma bangaskiya?

17 JAEL

“Mafi Albarka Ce Cikin Mata”

Ba za mu taɓa manta da irin ƙarfin zuciyar da Jael ta nuna saꞌad da ta ɗauki mataki a kan maƙiyin Jehobah ba. Me ya sa muke bukatar irin ƙarfin zuciyar da ta nuna sosai a yau?

18 GIDIYON

Ya Kasance da Ƙarfin Zuciya Kuma Ya Yi Taka Tsantsan

A waɗanne yanayoyi ne muke bukatar mu kasance da ƙarfin zuciya kuma mu yi taka tsantsan?

19 JEPHTHAH DA ꞌYARSA

Sun Cika Wani Alkawari Mai Wuya

Ta yaya misalin Jephthah da ꞌyarsa zai taimaka mana a yau?

20 SAMSON

Ya Roƙi Allah Ya Ƙarfafa Shi a Lokacin da Bai da Ƙarfi

Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Samson bayan da ya yi wani kuskure?

21 SAMA’ILA

Ɗan Yaron da Ya Yi Magana a Madadin Jehobah

A waɗanne yanayoyi ne yara za su bukaci ƙarfin zuciya don su yi abin da ya dace?

SASHE NA 2

SASHE NA 2

Daga Lokacin Sarakuna Zuwa Lokacin da Aka Sake Gina Urushalima

Wannan sashen na ɗauke da labaran mutane a dā da suka nuna bangaskiya da kuma ƙarfin zuciya. An soma da labarin Jonathan ɗan Sarki Shawulu, da Sarki Dauda, kuma an kammala da labarin Israꞌilawa lokacin da suka dawo daga bauta a Babila kuma suka sake gina Urushalima.

Sashe na 2 Lokacin da abubuwan suka faru

Hoton da ke nuna lokacin da wasu bayin Allah a Littafi Mai Tsarki suka rayu, da kuma wasu muhimman abubuwa da suka faru a lokacin sarakunan Israꞌilawa zuwa lokacin da aka sake gina Urushalima.

22 JONATAN

Ya Nuna Ƙarfin Zuciya don Ya Kasance da Aminci

Ta yaya Jonatan ya san wanda ya kamata ya kasance da aminci a gare shi? Ta yaya za mu yi koyi da shi?

23 DAUDA

Ya Yi Nasara a kan Wani Gwarzo

An san Dauda a matsayin “mai ƙarfin zuciya da kuma babban jarumi.” Ta yaya misalinsa ya taimaka ma wasu? Idan ka kasance da ƙarfin zuciya ta yaya hakan zai iya taimaka ma wasu?

24 ABIGAIL

Ta Fuskanci Mutane Biyu da Suke Fushi

Mene ne mazaje da matansu za su iya koya daga labarin Abigail?

25 DAUDA

Dauda Ya Yi Abin da Ya Dace da Ƙarfin Zuciya

Dauda ya sami damar ɗaukan fansa. Mene ne ya hana shi yin hakan? Ta yaya za mu iya bin misalinsa?

26 NATAN

Ya Yi wa Sarki Gyara

Mene ne muka koya daga labarin Natan game da yadda za mu taimaka wa abokinmu da ya yi zunubi mai tsanani?

27 MEFIBOSHET

Bai Yi Fushi Ba Saꞌad da Aka Yi Masa Rashin Adalci

Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga labarin Mefiboshet da za su iya karfafa mu?

28 ASA

Ya Bauta wa Jehobah Dukan Rayuwarsa

Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga wani mutum da ya bauta wa Jehobah dukan rayuwarsa?

29 ILIYA

Jehobah Ne Allahna

Me ya taimaka wa Iliya ya daina jin tsoro?

30 GWAURUWAR ZAREFAT

Ta Nuna Ƙarfin Zuciya a Lokaci Mai Wuya Sosai

Ta yaya labarinta zai taimaka mana mu dogara ga Jehobah?

31 WATA ƘARAMAR YARINYA ꞌYAR ISRAꞌILA

Ta Yi Magana Game da Allahnta da Ƙarfin Zuciya

Labarin ƙaramar yarinyar nan zai taimaka mana mu yi waꞌazi ko da muna jin tsoro.

32 ELISHA

“Ya Yahweh, . . . Ka Buɗe Idanunsa Ya Gani”

A waɗanne yanayoyin ne za mu sami ƙarfafa idan muka tuna cewa malaꞌiku suna tare da mu?

33 JEHOIADA

Ya Kāre Sarkin da Jehobah Ya Zaɓa

Mene ne Jehoiada ya yi da ya nuna cewa shi mai ƙarfin zuciya ne? Ta yaya za ka iya bin misalinsa?

34 HEZEKIYA

‘Ya Manne wa Jehobah’

Hezekiya ya nuna ƙarfin zuciya sosai da kuma bangaskiya. Ta yaya za mu bi misalinsa a yau?

35 MANASSE

Ya Nuna Ƙarfin Zuciya Kuma Ya Tuba

Me ya sa za mu iya cewa Manasse ya kafa misali mai kyau na nuna ƙarfin zuciya?

36 JOSIYA

Ya Taimaka wa Mutanen Su Sake Bauta wa Jehobah

Josiya ya jimre matsaloli saꞌad da yake tasowa. Ya kuma nuna ƙarfin zuciya duk da cewa mahaifinsa ya yi hamayya da bauta ta gaskiya. Ta yaya za mu yi koyi da misalinsa?

37 DANIYEL

Bai Yarda Ya “Ƙazantar da Kansa” Ba

A waɗanne hanyoyi ne matasa za su yi koyi da Daniyel wajen nuna ƙarfin zuciya da aminci? Ta yaya dukanmu za mu iya amfana daga labarinsa?

38 IBRANIYAWA UKU

Sun “Tsai da Ikon Wuta”

Ko a bakin mutuwa ma, Ibraniyawa ukun sun kasance da ƙarfin zuciya. Mene ne misalinsu zai iya koya mana game da sauƙin kai da rashin zafin rai da kuma aminci?

39 ESTA

“Idan Za a Kashe Ni, Bari a Kashe Ni”

Esta mace ce mai hikima da kuma biyayya. Shi ya sa mijinta ya saurare ta. Mene ne za mu iya koya daga misalinta?

40 NEHEMIYA

Ya Sake Gina Katangar

Mene ne misalin Nehemiya ya koya mana game da bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu? Ta yaya dattawa za su iya yin koyi da shi?

SASHE NA 3

SASHE NA 3

Daga Lokacin Almasihu Zuwa Lokacin Mabiyansa

Wannan sashen na ɗauke da labaran mutanen da suka nuna bangaskiya da ƙarfin zuciya a ƙarni na farko, har da wata budurwa Bayahudiya mai suna Maryamu. An kuma kammala da labarin manzo Yohanna.

Sashe na 3 Lokacin da abubuwan suka faru

Hoton da ke nuna lokacin da wasu bayin Allah a Littafi Mai Tsarki suka rayu da aka ambata a Sashe na 3. Yana kuma nuna wasu abubuwa masu muhimmanci da suka faru daga lokacin Almasihu zuwa ƙarshen rayuwar Manzo Yohanna.

41 ZAKARIYA DA ALISABATU

“Masu Adalci Ne a Gaban Allah”

Me ya sa Jehobah ya ɗauki Zakariya da Alisabatu a matsayin mutane masu adalci? Ta yaya za mu iya yin koyi da su?

42 MARYAMU

Ta Karɓi Aikin da Ƙarfin Zuciya

An ba wa Maryamu aiki mai wuya wanda ba a taɓa ba wa ɗanꞌadam ba. Ta yaya ta sami ƙarfin zuciya da ya taimaka mata ta iya yin aikin?

43 YUSUFU

Shi Uba ne Mai Ƙarfin Zuciya

Ta yaya ubanni a yau za su yi koyi da misali mai kyau da Yusufu ya kafa?

44 YOHANNA MAI BAFTISMA

‘Babu Wanda Ya Fi Shi Daraja’

Yohanna mutum ne mai ƙarfin zuciya da ya sauƙaƙa rayuwarsa. Ka karanta babin nan don ka ga abin da za mu iya koya daga wurinsa.

45 BITRUS

“Ni Mai Zunubi Ne”

Mene ne za mu iya koya daga wurin Bitrus game da ci-gaba da bauta ma Jehobah duk da kasawarmu?

46 MARYAMU MAGDALIN

“Na Ga Ubangiji!”

Maryamu ta yi amfani da duk abin da take da shi wajen taimaka wa Yesu da mabiyansa. Ta yaya za mu yi koyi da ita a nuna tausayi da kuma ƙarfin zuciya?

47 MARYAMU, ꞌYARꞌUWAR LIꞌAZARU

“Ta Yi Abin da Za Ta Iya Yi”

Yesu ya yaba wa Maryamu ꞌyarꞌuwar Liꞌazaru. A wace hanya ce ta nuna ƙarfin zuciya? Ta yaya za mu iya yin koyi da ita a yau?

48 ISTIFANUS

“Yana Cike da Ruhu Mai Tsarki da Bangaskiya”

Ana yi wa Istifanus shariꞌa, kuma a shariꞌar za a yanke shawara ko za a kashe shi ko a sake shi. Ta yaya ya kāre imaninsa? Ta yaya misalinsa zai taimaka mana mu ci-gaba da kasancewa da bangaskiya?

49 BITRUS

Ya Zama Dutse

Ta yaya misalin Bitrus zai taimaka mana mu dogara ga Jehobah saꞌad da muke jin tsoro?

50 SHAWULU DAGA TARSUS

Ya Canja Yadda Yake Tunani

Me ya sa mutumin da yake tsananta wa Kristoci sosai ya soma bauta wa Jehobah? Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga misalinsa?

51 BARNABAS

“Ɗan Taꞌaziyya”

Barnabas ya nuna ƙarfin zuciya ta wurin taimaka wa Shawulu da kuma kai shi wurin manzanni. Ta yaya za mu yi koyi da ƙarfin zuciyarsa kuma mu kasance a shirye mu taimaka ma wasu?

52 MARKUS

“Yana da Amfani Sosai Gare Ni”

Duk da cewa Markus ya rasa damar yin wani hidima na musamman, ya ci-gaba da taimaka wa ꞌyanꞌuwa da kuma bauta wa Jehobah da aminci. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarinsa?

53 BULUS

“Ina Roƙon Ku Ku Yi Ƙarfin Zuciya”

Ta yaya Bulus ya nuna ƙarfin zuciya a wani yanayi da kamar babu mafita? Ta yaya ƙarfin zuciya da ya nuna ya taimaka ma wasu?

54 MANZO YOHANNA

Ya Nuna Ƙarfin Zuciya a Lokuta Masu Wuya

Manzo Yohanna bai bar abubuwan da ya fuskanta su sa shi baƙin ciki ko tsoro ba. Ta yaya za mu bi misalinsa kuma mu ci-gaba da bauta wa Allah da ƙarfin zuciya?

KAMMALAWA

KAMMALAWA

“Ka Kasance da Ƙarfin Zuciya”

Littafi Mai Tsarki na ɗauke da labaran maza da mata, da yara da kuma tsofaffi da suka nuna ƙarfin zuciya kuma sun goyi bayan Jehobah. Labaransu za su iya taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya kamar yadda suka yi.

Yi hakuri, ba abin da ya dace da wanda kake nema.