Koma ka ga abin da ke ciki

Tunawa da Mutuwar Yesu

Sau daya a kowace shekara kuma a dubban wurare a fadin duniya, muna tunawa da mutuwar Yesu. Muna yin hakan ne domin ya umurci mabiyansa: ‘Ku rika yin haka domin tunawa da ni.’ (Luka 22:19) Za mu yi wannan taron a ranar:

Asabar, 31 ga watan Maris, 2018.

Muna gayyatar ka zuwa wannan taro na musamman. Kamar duka sauran taronmu, ana gayyatar kowa. Ba a biyan kudin kujera kuma ba a karban baiko.