Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Kamar Dai Ina da Kome da Nake So”

“Kamar Dai Ina da Kome da Nake So”
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1962

  • KASAR HAIHUWA: Kanada

  • TARIHI: Rayuwar da ba ta dace ba

RAYUWATA A DĀ

An haife ni a babban birnin Montreal da ke lardin Quebec a Kanada. Mu hudu ne iyayenmu suka haifa. Sun kula da mu sosai kuma sun rene mu a unguwar Rosemont. Mun ji dadin rayuwa a wurin.

Tun ina yaro na soma karanta Littafi Mai Tsarki. Na tuna lokacin da nake shekara 12, ina jin dadin karanta labarin Yesu a cikin Littafi Mai Tsarki. Yadda Yesu yake kaunar mutane da kuma tausaya musu ya burge ni sosai kuma hakan ya sa ina so na kasance da wannan hali. Amma hakan bai faru ba domin sa’ad da nake girma, na soma tarayya da abokan banza.

Mahaifina ya kware a busa sarewar da ake kira saxophone. Ya ba ni sarewarsa kuma ya koya min yadda ake waka kuma hakan ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwata. Saboda yadda nake son waka, na koyi yadda ake kada jita. Da shigewar lokaci, na hada kai da abokaina kuma muka soma rera waka a wurare da dama. Wasu furodusoshi a masana’antar waka sun ji dadin wakokina kuma suka ce za su so su taimaka mini don in yi suna. Na amince kuma na hada kai da wata babbar masana’antar waka. Wakokina sun yi kasuwa sosai kuma ana yawan sakawa a gidan rediyo da ke Quebec.

Kamar dai ina da kome da nake bukata. Ni matashi ne kuma na shahara sosai. Ina samu kudi sosai daga sana’ata. Idan gari ya waye, ina zuwa motsa jiki da wurin da za a gana da ni da sa wa mutane hannu a littattafansu kuma ana nuna ni a telibijin. Da daddare kuma ina rera wakoki a wurare da dama da kuma zuwa pati. Don na iya bi da mutane da yawa da suke so na, sai na soma shan giya sa’ad da nake matashi da shigewar lokaci na soma shan kwayoyi. Kari ga haka, ina yin abubuwan da ba su dace ba da kuma lalata sosai.

Wasu suna so su yi rayuwa irin nawa don suna ganin ina jin dadin rayuwa. Amma gaskiyar ita ce, ba na farin ciki sam musamman idan babu kowa tare da ni. Ina bakin ciki da kuma damuwa sosai. A daidai lokacin da nake samun daukaka a wannan harkar ne wasu furodusoshi guda biyu suka mutu sanadiyyar cutar kanjamau. Hakan ya ba ni mamaki! Ko da yake ina son waka sosai, na tsani irin rayuwar da nake yi.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

Duk da cewa na shahara, na san cewa akwai matsaloli sosai a duniyar nan. Me ya sa ake rashin adalci a ko’ina? Ban san dalilin da ya sa Allah bai dauki mataki ba don ya kawar da abubuwan nan. Nakan roki Allah ya sa in san dalilin da ya sa abubuwan nan suke faruwa. Da nake hutawa a lokacin da na je yin waka a wuraren dabam-dabam, sai na soma karanta Littafi Mai Tsarki. Ko da yake ban fahimci yawancin abin da nake karantawa ba, na gaya wa kaina cewa karshen duniyar nan ya kusa.

Da nake karanta Littafi Mai Tsarki ne na ga cewa Yesu ya taba yin azumi na kwana 40 a daji. (Matiyu 4:​1, 2) Na ce wa kaina zan yi azumi don watakila hakan zai sa Allah ya amsa addu’ata. Sai na zabi ranar da zan yi azumin. Makonni biyu kafin ranar azumin, Shaidun Jehobah guda biyu sun zo gidana kuma nan da nan na gaya musu su shigo su zauna. Na kalli daya daga cikin Shaidun mai suna Jacques kuma na ce masa, “Ta yaya za mu san cewa muna rayuwa a kwanaki na karshe?” Sai ya bude Littafin 2 Timoti 3:​1-5. Na yi musu tambayoyi da yawa kuma yadda suka yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen amsa duka tambayoyina ya burge ni sosai. Bayan wasu lokuta, sai na gane cewa ba na bukatar yin azumi kuma.

Na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidu a kai a kai. Jim kadan, na aske gashin da ke kaina kuma na soma halartar taro a Majami’ar Mulki. Yadda ’yan’uwan suka marabce ni ya kara tabbatar min da cewa wannan shi ne addinin na gaskiya.

Hakika, ina bukatar in yi wasu canje-canje a rayuwata don na bi ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Wasu daga ciki su ne, zan daina shan kwayoyi da kuma lalata. Kari ga haka, ina bukatar in so mutane fiye da yadda nake son kaina. Tun da ni kadai ne nake renon yarana, ina bukatar in koyi yadda zan kula da su da kuma koya musu yadda za su bauta wa Allah. Sai na bar sana’ata kuma na nemi aiki a wani kamfani da ake biya na karamin albashi.

Yin wadannan canje-canjen ba su da sauki. Na yi kokari wajen daina shan kwayoyi, amma na yi fama da matsalolin da ke tattare da daina shan kwayoyi. Kuma a wasu lokuta ina koma shan kwayoyin. (Romawa 7:​19, 21-24) Daina yin lalata ce ta fi min wuya. Ban da haka ma, sabon aikin da nake yi yana gajiyar da ni sosai kuma albashi da nake samu ba shi da yawa. Kudin da nake samu sa’ad da nake waka a cikin sa’o’i biyu shi ne albashina na wata uku.

Yin addu’a ya taimaka min in yi wadannan canje-canjen masu wuya. Karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai ma ya amfane ni sosai. Akwai wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka karfafa ni. Littafin 2 Korintiyawa 7:1 ta karfafa mu cewa, “mu tsabtace kanmu daga dukan abin da zai sa jiki da zuciyarmu ya ƙazantu.” Wani littafi kuma da ya taimaka min na fahimci cewa zan iya canja halayena marasa kyau shi ne Filibiyawa 4:13. Ayar ta ce: ‘Zan iya yin kome ta wurin [Allah] wanda yake ƙarfafa ni.’ Jehobah Allah ya amsa addu’ata kuma ya taimaka min na fahimci kuma in bi koyarwar da ke Littafi Mai Tsarki. Hakan kuma ya sa na yi wa Jehobah alkawarin bauta masa. (1 Bitrus 4:​1, 2) Na yi baftisma a shekara ta 1997.

YADDA NA AMFANA

Ina da tabbacin cewa da a ce na ci gaba da irin rayuwar da nake yi a dā, da yanzu na mutu. Amma yanzu ina rayuwa mai ma’ana! Matar da na aura mai suna Elvie ta taimaka mini sosai. Muna hidimar majagaba muna koya wa mutane Littafi Mai Tsarki tare. Hakan na sa ni farin ciki sosai. Ina yi wa Jehobah matukar godiya don yadda ya taimaka min in kusace shi.​—Yohanna 6:44.