Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Akwai Abubuwa da Dama da Na So In Sani”

“Akwai Abubuwa da Dama da Na So In Sani”
  • Shekarar Haihuwa: 1976

  • Ƙasar Haihuwa: Honduras

  • Tahiri: Fasto

RAYUWATA A DĀ

An haife ni a birnin La Ceiba da ke Honduras, ni kadai ne namiji kuma ni ne auta cikin yara biyar da iyayena suka haifa. Ni ne kadai kurma a iyalinmu. Ana yawan aikata laifi a wurin da muke zama, kuma mu talakawa ne sosai. Da nake dan shekara hudu, abubuwa sun dada mana wuya bayan mahaifina ya fado sa’ad da yake aiki a kan wani rufin gida kuma ya mutu.

Mahaifiyata ta yi kokari ta kula da mu, amma da kyar take samun kudi ta saya min riguna. A duk lokacin da aka yi ruwa, sanyi yana kama ni sosai don ba ni da rigar sanyi.

Yayin da nake girma, na koyi Yaren Kurame na Honduras (LESHO), don in iya tattaunawa da kurame kamar ni. Da yake Mahaifiyata da ’yan’uwana ba su iya Yaren Kurame na Honduras ba, suna kokari su yi magana da ni ta wurin amfani da yaren kuramen da suka kirkiro da kansu. Duk da haka, mahaifiyata tana kaunata sosai kuma ta kāre ni daga abubuwan da za su jawo min lahani. Ta yi kokari ta gargade ni in guji shan taba da kuma yin tilis da giya. Hakan ya sa ban zama mai shaye-shaye ko dan kwaya ba.

Sa’ad da nake karami mahaifiyata takan kai ni Cocin Katolika, amma ban fahimci abin da ake yi a wurin ba don ba wanda yake fassara min abin da ake fada zuwa yaren kurame. Na bi na gaji da zuwa cocin, da na kai shekara goma sai na daina zuwa. Duk da haka, a zuciyata na so in san abubuwa da yawa game da Allah.

Da na kai shekara 23 a 1999, na hadu da wata mata ’yar cocin evangelika da ta fito daga Amirka. Ta koya min wasu abubuwa daga Littafi Mai Tsarki kuma ta koya min Yaren Kurame na Amirka (ASL). Na ji dadin abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki har na yanke shawara zan zama fasto. Don haka, na kaura zuwa kasar Puerto Rico don in kara ilimi a makarantar kurame na Kiristoci. Da na dawo garinmu La Ceiba a 2002, sai wasu abokaina suka taimaka min na kafa coci. Daga baya na auri daya daga cikinsu mai suna Patricia.

A matsayina na faston cocin, nakan yi wa’azi a cocin da Yaren Kurame na Honduras, in nuna musu hotunan labaran da ke Littafi Mai Tsarki, har in yi wasan kwaikwayon labaran don in taimaka wa kuramen su fahimta. Nakan kuma ziyarci kuramen da suke garuruwan da ke kusa da mu in karfafa su kuma in taimaka musu. Har na je wa’azi a kasar Amirka da Zambiya. Amma a gaskiya, ban fahimci abubuwa da yawa a Littafi Mai Tsarki ba. Abin da aka gaya min da kuma abin da na fahimta daga hotunan ne kawai na koya wa mutane. A gaskiya akwai abubuwa da dama da na so in sani.

Wata rana, wasu membobin cocin suka soma yada karya game da ni. Sun ce ni mashayi ne kuma ina yin zina. Abin ya bata min rai sosai. Ba da dadewa ba, ni da matata mun bar cocin.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

Shaidun Jehobah suna yawan zuwa gidanmu, amma ni da matata Patricia korar su muke yi. Bayan da muka bar zuwa cocinmu, Patricia ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu ma’aurata da Shaidun Jehobah ne. Sunansu Thomas da Liccy. Yadda suke yaren kurame duk da cewa su ba kurame ba ne ya burge ni. Don haka, ni ma na yarda su yi nazari da ni.

Mun yi ’yan watanni muna nazari da bidiyoyin Yaren Kurame na Amirka. Amma, da wasu abokanmu suka ce Shaidun Jehobah ba sa bin Kristi, mutane ne suke bi, sai muka daina nazarin. Ko da yake Thomas ya nuna min abubuwan da suka tabbatar cewa Shaidun Jehobah ba su da shugabanni ’yan Adam, ban yarda da shi ba.

’Yan watanni bayan haka, Patricia ta soma ciwon bakin ciki mai tsanani, kuma ta yi addu’a Allah ya sake turo Shaidun Jehobah gidanmu. Ba da dadewa ba, wata makwabciyarmu Mashaidiyar Jehobah ta zo wurin Patricia kuma ta ce za ta gaya wa Liccy ta kawo mata ziyara. Liccy ta taimaka mata sosai. Ta yi ta zuwa kowane mako don ta karfafa Patricia kuma ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Duk da haka, ban yarda da Shaidun Jehobah ba.

A shekara ta 2012, Shaidun Jehobah sun yi wa’azi na musamman don su rarraba bidiyon nan, Za Ka so ka San Amsoshin Wadannan Tambayoyin? a Yaren Kurame na Honduras. Liccy ta kawo mana namu faifan bidiyon. Da na kalli bidiyon, na ga cewa abubuwa da yawa da na koya wa mutane a dā, kamar koyarwar wutar jahannama da kurwa marar mutuwa, ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. Hakan ya ba ni mamaki sosai.

Bayan ’yan kwanaki, na je wurin taron Shaidun Jehobah don in yi magana da Thomas. Na gaya masa cewa ina so in dinga koya wa kurame gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba tare da na zama Mashaidin Jehobah ba. Na so ne in kafa wani sabon cocin kurame. Thomas ya yaba min don matakin da nake shirin daukawa amma ya nuna min abin da ke Afisawa 4:​5, inda ya nuna cewa wajibi ne Kiristoci na gaskiya su kasance da hadin kai.

Kari ga haka, Thomas ya ba ni bidiyon nan Jehovah’s Witnesses​—⁠Faith in Action, Part 1: Out of Darkness na Yaren Kurame na Amirka. Bidiyon ya nuna yadda wasu mutane suka bincika Littafi Mai Tsarki don su fahimci gaskiya game da wasu abubuwan da ake koyarwa. Na gane abin da ya sa mutanen suka yi wannan binciken domin ni ma na so in san gaskiya. Bidiyon ya sa na amince cewa abin da Shaidun Jehobah suke koyarwa gaskiya ne, domin dukan koyarwarsu daga Littafi Mai Tsarki ne. Sai na sake yin nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma ni da Patricia muka yi baftisma a 2014, muka zama Shaidun Jehobah.

YADDA NA AMFANA

Ina son Shaidun Jehobah domin suna da dabi’u masu kyau da suka dace da bayin Allah. Suna yin magana da kuma tarayya da mutane yadda ya dace. Suna zaman lafiya da kuma karfafa juna. Shaidun Jehobah suna da hadin kai kuma abu daya suke koyarwa ko da wace kasa suka fito ko wane yare suke yi.

Na ji dadi da na koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, na gane cewa Jehobah shi ne Allah Mai Iko Duka. Yana kaunar kurame da wadanda ba kurame ba. Ina godiya don irin kaunar da Allah ya nuna min. Na kuma koya cewa duniya za ta zama aljanna kuma za mu sami damar yin rayuwa har abada cikin jin dadi da kuma koshin lafiya. Ina marmarin ganin lokacin da abubuwan nan za su faru.

Ni da Patricia muna jin dadin tattauna Littafi Mai Tsarki da kurame. Yanzu muna nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu membobin cocinmu na dā. Amma yanzu ba na shakkar abin da nake koyarwa kamar yadda na yi a lokacin da ni fasto ne. Nazarin Littafi Mai Tsarki da na yi da Shaidun Jehobah ya sa na sami amsoshin dukan tambayoyin da nake da su.