Koma ka ga abin da ke ciki

’Yan Sanda Sun Raka Joseph

’Yan Sanda Sun Raka Joseph

Idan kai Mashaidin Jehobah ne, yaya za ka ji idan ’yan sanda suka raka ka yin wa’azi gida-gida? Abin da ya faru da Joseph a kasar Micronesia a shekara ta 2017 ke nan. Dan’uwan tare da wasu ’yan’uwa uku sun je wa’azi na musamman a wani tsibiri.

’Yan’uwan nan hudu sun iso wani karamin tsibiri da rana kuma mutane wajen 600 ke zama a wurin. Magajin garin ya marabce su sa’ad da suka isa tsibirin. Joseph ya bayyana abin da ya faru ya ce: “Magajin garin ya gaya mana cewa motar ’yan sanda za ta kai mu dukan gidajen da ke garin. Abin da ya ce ya burge mu kuma mun gode masa sosai, amma ba mu amince da hakan ba. Muna so mu je gidan mutane yin wa’azi yadda muka saba ba tare da ’yan sanda sun raka mu ba.”

Sai masu shelar suka soma tafiya da kafa don su yi wa mutane da yawa wa’azi. Shaidun sun ce: “Mutanen sun nuna mana karimci sosai kuma sun saurari sakonmu. A sakamakon haka, mun dau lokaci fiye da yadda muka yi zato a duk gidan da muka je.”

Daga baya, motar ’yan sanda ta wuce Joseph sau uku sai ’yan sandan suka tsaya. Sun tambayi Joseph ko zai so su kai shi sauran gidajen da yake so ya je wa’azi. Joseph Ya ce a’a, amma a wannan karon sun nace kuma suka ce masa, ‘Lokacin da ya rage muku bai da yawa, don haka, za mu kai ka sauran gidajen.’ Ba zan iya kin amincewa da abin da suka ce ba, domin har ila gidajen da zan je wa’azi suna da yawa. Yayin da muke kusantar gidajen, ’yan sandan suna gaya mini sunayen masu gidan kuma sun gaya mini cewa idan na kwankwasa kuma babu wanda ya amsa, za su hura hon na motarsu don masu gidan su fito.

Joseph ya ce: “Da taimakon ’yan sandan, mun ziyarci dukan gidajen a ranar. Kari ga haka, mun ba mutane da yawa littattafai kuma muka gaya wa wadanda suke son yin nazari cewa za mu komo.”

’Yan sandan sun gaya wa Joseph cewa “sun ji dadin yin wa’azi.” Da yamma sa’ad da Shaidun suke barin tsibirin, ’yan sandan sun yi musu ban-kwana suna murmushi kuma suna rike da littattafanmu a hannunsu.