Koma ka ga abin da ke ciki

Ki Gaya Masu Cewa Kina Kaunar Su

Ki Gaya Masu Cewa Kina Kaunar Su

Ong-li wata Mashaidiya ce a kasar Bulgariya. Ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata mai suna Zlatka duk da cewa maigidan matar ba ya nazarin tare da su. Ong-li ta ce: “Sa’ad da muke nazari a kan batun nuna kauna a iyali, na nanata muhimmancin gaya wa abokan aurenmu da kuma ’ya’yanmu cewa muna kaunar su. Sai Zlatka ta kalle ni da bakin ciki ta ce ba ta taba gaya wa maigidanta ko ’yarta ’yar shekara tara cewa tana kaunar su ba!”

Zlatka ta kara da cewa, “Ina a shirye in yi kome-da-kome dominsu, amma ba zan iya gaya masu cewa ina kaunar su ba.” Ta kara cewa: “Mahaifiyata ba ta taba ce min tana kauna ta ba, kuma kakata ba ta taba gaya wa mamata cewa tana kaunar ta ba.” Amma Ong-li ta nuna wa Zlatka cewa Jehobah ya furta da bakin sa cewa yana kaunar Yesu. (Matiyu 3:17) Don haka, ta karfafa Zlatka ta yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mata ta iya gaya wa maigidanta da ’yarta cewa tana kaunar su.

Ong-li ta ce: “Bayan kwana biyu, Zlatka ta gaya min da farin ciki cewa ta yi addu’a don Jehobah ya taimaka mata. Kuma da maigidanta ya dawo gida, sai ta gaya masa cewa ta koya daga Littafi Mai Tsarki cewa yana da muhimmanci mace ta kasance mai biyayya kuma ta kaunaci mijinta. Bayan haka, ta dan dakata, sai kuma ta gaya masa cewa tana kaunar shi sosai. Sa’ad da ’yarta ta dawo gida sai Zlatka ta rungume ta kuma ta gaya mata cewa tana kaunar ta. Zlatka ta gaya min cewa: ‘Yanzu ina farin ciki. A shekarun baya, ban iya furta abin da ke zuciyata ba, amma da taimakon Jehobah yanzu, ina iya nuna wa iyalina cewa ina kaunar su.’

Ong-li ta ci gaba da gayyatar mutanen unguwarsu su yi nazarin Littafi Mai Tsarki

Ong-li ta ce: “Bayan mako daya, na hadu da maigidan Zlatka kuma ya gaya min cewa ‘mutane da yawa sun ce in hana Zlatka yin nazarin Littafi Mai Tsarki amma da alama cewa nazarin da take yi yana amfanar iyalinmu. Yanzu muna farin ciki sosai kuma muna da dangantaka mai kyau.’”