Koma ka ga abin da ke ciki

Kuna Aikin Wa’azi a Kasan Waje Kuwa?

Kuna Aikin Wa’azi a Kasan Waje Kuwa?

E. A duk inda muke, Shaidun Jehobah suna kokarin su kasance da hali na mai wa’azi a kasan waje, kullum muna gaya wa mutane da muke gamu da su game da bangaskiyar da muke da shi.​—Matta 28:19, 20.

Ban da haka, wasu Shaidu suna zuwa wasu wurare ko kuma su kaura su koma kauyensu inda mutane ba su riga sun ji bisharar Littafi Mai Tsarki ba. Wasu Shaidu kuma suna kaura zuwa kasashen waje don su iya wa’azi wa mutane da yawa. Suna farin cikin sa hannu a cika wannan annabci da Yesu ya ce: “Za ku zama shaiduna ... har kuma iyakan duniya.”​—Ayyukan Manzanni 1:8.

Mun kafa wata makaranta a shekara ta 1943, don ta koyar da wadanda suke son su je aikin wa’azi a kasashen waje. Tun daga lokacin an sami Shaidu fiye da 8,000 da suka je wannan makarantar da ake kira Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead.