Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ake Kiranku Shaidun Jehobah?

Me Ya Sa Ake Kiranku Shaidun Jehobah?

 A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah shi ne sunan Allah. (Fitowa 6:3; Zabura 83:18) Mashaidi mutum ne da yake sanar da ra’ayoyi ko kuma gaskiya da ya tabbatar da su.

 Saboda haka, sunanmu Shaidun Jehobah yana nuna cewa mu rukunin Kiristoci ne da suke sanar da gaskiya game da Jehobah, Mahaliccin dukan abubuwa. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Muna ba da shaida ga mutane ta wurin yadda muke rayuwa da kuma ta wurin gaya musu abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki.—Ishaya 43:10-12; 1 Bitrus 2:12