Koma ka ga abin da ke ciki

Ku Kiristoci ne Kuwa?

Ku Kiristoci ne Kuwa?

 E. Mu Kiristoci ne. Ga dalilan nan:

  •   Muna ƙoƙarin bin koyarwa da halayen Yesu Kristi a tsanake.—1 Bitrus 2:21.

  •   Mun gaskata cewa Yesu shi ne hanyar ceto “babu wani suna ƙarƙashin sama, da aka bayar wurin mutane, inda ya isa mu tsira.”—Ayyukan Manzanni 4:12.

  •   Sa’an da mutum ya zama Mashaidin Jehobah, akan yi masa baftisma cikin sunan Yesu.—Matta 28:18, 19.

  •   Muna yin addu’a cikin sunan Yesu.—Yohanna 15:16.

  •   Mun gaskata cewa Yesu shi ne Shugaba, ko kuma wanda aka ba wa iko, akan kowane mutum.—1 Korinthiyawa 11:3.

 Amma, dabam muke da sauran rukunonin addinai da ake ce da su Kiristoci a hanyoyi da yawa. Alal misali, mun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Yesu Ɗan Allah ne, ba ɓarin Allah-Uku-Cikin Ɗaya ba. (Markus 12:29) Ba mu gaskata cewa kurwa marar mutuwa ce ba, babu wani dalili cikin Nassi da ya ce Allah zai yi wa mutane azaba cikin jahannama, ko kuma cewa a ba waɗanda suke ja-gora cikin addinai lakabi da zai ɗora su fiye da wasu ba.—Mai Wa’azi 9:5; Ezekiel 18:4; Matta 23:8-10.