Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ba A Kiran Wajen Taronku Coci?

Me Ya Sa Ba A Kiran Wajen Taronku Coci?

 A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar Hellenanci da a kan fassara zuwa “coci” wani lokaci, tana nufin taron mutane masu ibada ne ba majami’ar da ake yin ibadar ba.

 Ka yi la’akari da wannan misalin: Sa’ad da manzo Bulus ya rubuta wasika zuwa ga Kiristoci da ke Roma, bayan ya aika gaisuwa ga Akila da Biriska sai ya dada cewa: “Ku kuma gai da ikilisiyar [coci] da ke taruwa a gidansu.” (Romawa 16:5, Littafi Mai Tsarki) Bulus bai aika da gaisuwarsa zuwa ga ginin ba, amma ga mutanen ne, wato wadanda da ke taruwa a gidan. a

 Saboda haka, maimakon a kira wajen da muke ibada coci, muna kiransa “Majami’ar Mulki.”

Me ya sa muke kiransa “Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah”?

 Ga wasu dalilan da suka sa wannan sunan ya dace:

  •   Ginin yana kama da majami’a ko kuma wajen taro.

  •   Muna taruwa a wurin don mu yi wa Jehobah sujjada, wanda ya yi tanadin Littafi Mai Tsarki, kuma muna ba da shaida game da shi.​—Zabura 83:18; Ishaya 43:12.

  •   Muna kuma taruwa don mu koya game da Mulkin Allah, wanda Yesu ya yi wa’azinsa sau da sau.​—Matta 6:9, 10; 24:14; Luka 4:43.

 Muna gayyatarka zuwa Majami’ar Mulkin da ya fi kusa da kai don ka ga yadda Shaidun Jehobah suke gudanar da taronsu.

a An yi wasu kalamai makamancin haka a 1 Korintiyawa 16:19; Kolosiyawa 4:15; da kuma Filimon 2.