Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Shaidun Jehobah ’Yan Furotesta Ne?

Shaidun Jehobah ’Yan Furotesta Ne?

A’a. Shaidun Jehobah Kiristoci ne, amma mu ba ’yan Furotesta ba ne. Me ya sa?

Addinin Furotesta “addini ne da ke hamayya da addinin Katolika.” Ko da yake Shaidun Jehobah ba su yarda da koyarwar Cocin Katolika ba, mu ba Furotesta ba ne domin wadannan dalilan:

  1. Abubuwa da yawa da ’yan Furotesta suka yi imani da su ba su yi daidai da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah daya” ne, ba allah-uku-cikin daya ba. (1 Timotawus 2:5; Yohanna 14:28) Kuma ya ce Allah zai hallaka miyagu har abada, maimakon ya jefa su cikin jahannama.Zabura 37:9; 2 Tasalonikawa 1:9.

  2. Ba ma yin hamayya da cocin Katolika ko wani coci dabam kuma ba ma kokarin kyautata su. Akasin haka, muna wa’azin bisharar Mulkin Allah kuma muna kokarin taimaka wa mutane su ba da gaskiya ga Allah. (Matta 24:14; 28:19, 20) Muna sha’awar koya wa mutane gaskiya game da Allah da kuma Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki, ba don mu kyautata wani addini ko kuma rukuni ba.Kolosiyawa 1:9, 10; 2 Timotawus 2:24, 25.