Koma ka ga abin da ke ciki

Kuna Ba da Zakka Kuwa?

Kuna Ba da Zakka Kuwa?

 A’a, Shaidun Jehobah ba sa ba da zakka; amma suna goyon bayan aikinmu ta wurin ba da gudummawa na son rai ba tare da an ambata sunan wanda ya bayar ba. Mene ne zakka, kuma me ya sa Shaidun Jehobah ba sa ba da zakka?

 A cikin Dokar da aka ba wa al’ummar Isra’ila ta dā an ba da doka a ba da zakka ko kuma a kawo kashi goma daga mallakar da mutum yake da shi. Amma Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa wannan dokar ta hada da a “karbi ushira daga wurin mutane” bai shafi Kiristoci ba.​—Ibraniyawa 7:​5, 18; Kolosiyawa 2:​13, 14.

 Maimakon ba da zakka, Shaidun Jehobah suna yin koyi ne da Kiristoci na farko kuma suna goyon bayan hidimarsu a hanyoyi biyu: ta wurin yin wa’azi da koyarwa da kuma ba da gudummawar kudi da son rai.

 Saboda haka, muna bin ja-gorar Littafi Mai Tsarki ne ga Kiristoci: “Kowane mutum ya aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da dadin rai.”—2 Korintiyawa 9:7.