Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Nazarin Littafi Mai Tsarki?

Mene ne Nazarin Littafi Mai Tsarki?

Shaidun Jehobah suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki dake amsa tambayoyi masu yawa, kamar su:

  • Wane ne Allah?

  • Allah yana kula da mu kuwa?

  • Ta yaya zan daidaita aurena?

  • Ta yaya zan iya samun farin ciki a rayuwata?

A kasa za ka sami amsoshin tambayoyin da aka yi game da shirin nazarin Littafi Mai Tsarki.

Yaya ake yin nazarin? Muna ɗaukan jigogi game da “Allah” ko kuma “aure” sai mu bincika ayoyi dabam dabam da suka shafi jigon nan. Idan muka kwatanta su za mu ga abin da Littafi Mai Tsari ya ce game da jigon, kuma ta hakan za mu bari Littafi Mai Tsarki ya bayyana kansa.

Don mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki, muna amfani da Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Wannan littafin yana bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Allah, Yesu, da kuma nan gaba.

Nawa ne ake biya idan za a yi nazarin Littafi Mai Tsarki? Ba a biyan ko sisi idan za a yi nazarin ko kuma littafin da ake nazari ta ita.

Mene ne tsawon nazarin? Yawancin mutane suna keɓe awa ɗaya ko fiye da haka a kowane mako don mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Ba dole ba ne sai an yi nazari na awa ɗaya ba. Za mu yi nazarin a duk lokacin da ka ba mu.

Mai zai faru idan na ce a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni? Idan ka ce a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai, ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah zai ziyarce ka a lokaci da kuma wurin da ka zaɓa. Zai ko zata ɗauki mintoci kaɗan don su nuna maka yadda muke yin nazari. Idan kana so, sai ka ci gaba.

Idan na yarda da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, dole ne sai na zama ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah? A’a. Shaidun Jehobah suna son su koya wa mutane game Littafi Mai Tsarki, amma ba mu tilasta wa mutane su bi addininmu. Maimakon haka, muna nuna masu abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, kuma fahimci cewa kowane mutum zai iya zaɓan abin da ya yi imani da shi.—1 Bitrus 3:15.