Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ba Ku Yin Bikin Ista?

Me Ya Sa Ba Ku Yin Bikin Ista?

Kurakure da Ake Yawan Yi

Kage: Dalilin da ya sa Shaidun Jehobah ba sa bikin Ista shi ne domin su ba Kiristoci ba ne.

Gaskiya: Mun gaskata cewa Yesu Kristi ne mai Cetonmu, kuma muna iyakacin kokarinmu mu bi “sawunsa” yadda ya kamata.—1 Bitrus 2:21; Luka 2:11.

Kage: Ba ku gaskata cewa an ta da Yesu daga matattu ba.

Gaskiya: Mun gaskata da tashin Yesu daga matattu; mun sani cewa shi ne tushen bangaskiyar Kirista kuma muna nanata wannan cikin wa’azin da muke yi.—1 Korintiyawa 15:3, 4, 12-15.

Kage: Ba ku damu ba cewa yaranku ba sa moran hutun Ista.

Gaskiya: Muna kaunar yaranmu, muna ba da lokaci sosai a renonsu kuma muna taimaka musu su kasance da farin ciki.—Titus 2:4.

Me ya sa Shaidun Jehobah ba sa yin bikin Ista?

  • Hutun bikin Ista ba shi da tushe cikin Littafi Mai Tsarki.

  • Yesu ya ce mu tuna da mutuwarsa, ba tashinsa daga matattu ba. Muna yin hakan kowace shekara daidai da kwanan wata na kalandar Yahudawa.—Luka 22:19, 20.

  • Allah bai yarda da Ista ba domin tushensa daga al’adu na bukukkuwan ni’ima na dā ne. Allah ya bukaci mu bauta masa ‘shi kadai,’ domin ba ya son mu hada sujjada da muke masa da ayyuka da bai amince da su ba.—Fitowa 20:5; 1 Sarakuna 18:21.

Mun tabbata cewa muna da kwararren dalili na kin yin bikin Ista daga cikin Littafi Mai Tsarki da yake karfafa mu mu yi amfani da “sahihiyar hikima da hankali” maimakon mu bi al’adu kawai. (Misalai 3:21; Matta 15:3) Ko da yake muna ba wa mutane amsar tambayar da suke yi game Ista, duk da haka muna daraja imanin mutane.—1 Bitrus 3:15.