Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ba Ku Yaki?

Me Ya Sa Ba Ku Yaki?

 Ga dalilan da ya sa Shaidun Jehobah ba sa yaki:

  1.   Biyayya ga Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce bayin Allah za su “bubbuge takubansu su zama garmuna” kuma ba za su “kara koyon yaki nan gaba ba.”—Ishaya 2:4.

  2.   Biyayya ga Yesu. Yesu ya ce wa manzo Bitrus: “Mayar da takobinka gidansa: gama dukan wadanda suka dauki takobi, da takobi za su lalace.” (Matta 26:52) Ta haka, Yesu ya nuna cewa mabiyansa ba za su kasance da makaman yaki ba.

     Mabiyan Yesu suna biyayya da wannan umurni na kasance ‘ba na duniya ba’ ta wurin kin sa hannu a siyasa. (Yohanna 17:16) Ba sa zanga-zanga da sojoji ko kuma su hana wadanda suke son shigar soja shiga ba.

  3.   Kaunar juna. Yesu ya umurci almajiransa su “yi kaunar juna.” (Yohanna 13:34, 35) Haka ne suke yi cikin taron ’yan’uwa na dukan kasashe inda babu wanda yake yaki da dan’uwansa ko ’yar’uwarsa.—1 Yohanna 3:10-12.

  4.   Misalin Kiristoci na farko. Encyclopedia of Religion and War ya ce: “Mabiyan Yesu na farko sun ki yaki da shigar soja,” domin sun sani cewa wadannan ayyuka ba su “jitu da dokar da Yesu ya bayar cewa a yi kaunar juna kuma cewa mutum ya yi kaunar magabcinsa” ba. Haka ma, malamin addini dan Jamus, Peter Meinhold ya ce game da almajiran Yesu na farko: “Kirista ba zai zama soja ba.”

Yadda suke taimaka wa mutane

 Shaidun Jehobah mutane ne masu son zaman lafiya, ba sa jawo tashin hankali a duk kasar da suke. Muna biyayya da gwamnati daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya fada:

  •   “Yi zaman biyayya da ikon masu-mulki.”—Romawa 13:1.

  •   “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah.”—Matta 22:21.

 Saboda haka, muna biyayya ga dokoki, muna biyar haraji, kuma muna goyon bayan gwamnati wajen kokarinsu na gyara zaman jama’a.