E. Dukan Shaidun Jehobah masu wa’azi ne, ko kuma masu hidima, har da miliyoyin mata. Yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa, “Mata masu-shelar bisharan kuwa babbar runduna ne.”Zabura 68:11.

Mata da Shaidun Jehobah ne suna bin misalin abin da mata cikin Littafi Mai Tsarki suka yi ne. (Misalai 31:10-31) Ko da yake ba su da matsayi na shugabanci cikin ikilisiya, suna wa’azi sosai ga jama’a. Suna kuma koya wa yaransu ka’idodi na Littafi Mai Tsarki. (Misalai 1:8) Mata da Shaidun Jehobah ne suna kokari su kasance da halin kirki a furucinsu, da kuma ayyukansu.Titus 2:3-5.