Koma ka ga abin da ke ciki

Kuna Yarda a Yi Muku Maganin Jinya Kuwa?

Kuna Yarda a Yi Muku Maganin Jinya Kuwa?

E, Shaidun Jehobah suna karban magani kuma suna yarda a yi musu jinya. Ko da yake muna kokarin mu kula da kanmu don mu kasance da lafiya, a wani lokaci muna bukatar “mai magani.” (Luka 5:31) Luka da ya yi rayuwa a karni na farko likita ne, kuma haka ma a yau, wasu cikin Shaidun Jehobah likitoci ne.—Kolosiyawa 4:14.

Idan jinya ta saba wa ka’idodin Littafi Mai Tsarki, ba ma yi. Alal misali, ba ma yarda da karin jini don yin jinya saboda Littafi Mai Tsarki ya haramta yin hakan. (Ayyukan Manzanni 15:20.) Littafi Mai Tsarki ma ya haramta jinya da ake hadawa da tsafi.—Galatiyawa 5:19-21.

Amma, yawancin magunguna da ake amfani da su ba su saba da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, kowa yana bukata ya tsai da shawarar kansa. Wani Mashaidi zai iya yarda da wata jinya, amma kuma wani ya ki da irin jinyar.—Galatiyawa 6:5.