Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Yadda Shaidun Jehobah Suke Yin Jibin Ubangiji Ya Bambanta da Na Sauran Addinai?

Me Ya Sa Yadda Shaidun Jehobah Suke Yin Jibin Ubangiji Ya Bambanta da Na Sauran Addinai?

Muna kokarin bin abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da tunawa da Mutuwar Yesu, wanda ake ce da shi “Jibin Ubangiji.” (1 Korintiyawa 11:20) Akasin haka, darikoki da yawa ba sa bin abin da Littafi Mai Tsarki ya fadi game da yadda ya kamata a yi Jibin Ubangiji.

Manufa

Manufar Jibin Ubangiji shi ne mu tuna da Yesu domin mu yi godiya saboda hadayar da ya yi a madadinmu. (Matta 20:28; 1 Korintiyawa 11:24) Wannan abin tunin ba wata al’ada da ke kawo wa mutum farin jini a gaban Allah ko kuma sa a gafarta masa zunubansa ba. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa za a iya gafarta zunubanmu ta wajen imani da Yesu, ba ta wurin wata al’ada ba.—Romawa 3:25; 1 Yohanna 2:1, 2.

Sau nawa ya kamata a yi jibin?

Yesu ya gaya wa almajiransa su rika tuna da Jibin Ubangiji, amma bai fada musu sau nawa za su rika yinsa ba. (Luka 22:19) Wasu suna yinsa sau daya a wata, wasu sau daya a mako, wasu kuma sau daya a rana ko fiye da haka ko kuma duk yadda mutum ya ga dama. * Amma akwai abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su game da wannan batun.

Yesu ya kafa Jibin Ubangiji a ranar Idin Ketarewa na Yahudawa kuma a ranar ne ya mutu. (Matta 26:​1, 2) Kuma hakan ya faru kamar yadda aka kayyade domin Littafi Mai Tsarki ya kwatanta hadayar Yesu da hadayar Dan Rago na Idin Ketarewa. (1 Korintiyawa 5:7, 8) Ana yin Idin Ketarewa sau daya ne a shekara. (Fitowa 12:1-6; Levitikus 23:5) Hakazalika, Kiristoci na farko sun yi Jibin Ubangiji sau daya a shekara kuma Shaidun Jehobah ma suna bin wannan misalin.

Rana da kuma lokacin da ya kamata a yi jibin

Yadda Yesu ya kafa Jibin Ubangiji ya taimaka mana mu san ko sau nawa a shekara ya kamata mu tuna mutuwarsa da lokaci da kuma kwanan watan da ya kamata mu yi hakan. Ya yi jibin bayan faduwar rana a ranar 14 ga Nisan shekara ta 33, bisa ga kirgen kwanan watan Yahudawa na dā. (Matta 26:18-​20, 26) Muna yin jibin a wannan ranar kowace shekara kamar yadda Kiristoci na farko suka yi. *

Ko da yake 14 ga Nisan, shekara ta 33 ya fadi ne a ranar Jumma’a, wannan kwanan watan tana iya faduwa a wata rana dabam a kowace shekara. Muna sanin ranar 14 ga Nisan ta wajen bin hanyar kirgen kwanan wata da aka yi amfani da shi a zamanin Yesu.

Gurasa da giya

Yesu ya yi amfani da gurasa marar yisti da kuma jar giya da ya rage bayan sun yi Idin Ketarewa. (Matta 26:26-28) Muna bin misalinsa ta wajen amfani da gurasa marar yisti da kuma asalin jar giya da ba a saka kome a ciki ba, ba ruwan ’ya’yan itacen inabi da aka hada masa kayan zaki ba.

Wasu darikoki suna amfani da gurasa mai yisti, amma a cikin Littafi Mai Tsarki akan yi amfani da yisti a alamta zunubi da aibi. (Luka 12:1; 1 Korintiyawa 5:6-8; Galatiyawa 5:7-9) Saboda haka, gurasa da babu yisti ne ya dace a yi amfani da shi a alamci jiki marar zunubi na Kristi. (1 Bitrus 2:22) Littafi Mai Tsarki bai yarda a yi amfani da ruwan ’ya’yan itacen inabi a matsayin jar giya ba. Amma wasu cococi suna amfani da shi domin sun hana shan giya.—1 Timotawus 5:23.

Gurasar da giyar ba jikinsa da kuma jininsa na zahiri ba

Gurasa da kuma jar giya da ake yin amfani da su a lokacin Jibin suna wakiltar jikin Kristi da kuma jininsa. Ba sa juyawa su zama jikinsa da kuma jininsa a zahiri kamar yadda wasu suke gani. Ga wasu hujjoji da ya kamata mu yi la’akari da su.

  • Da a ce Yesu ya gaya wa almajiransa su sha jininsa, da hakan yana nufin cewa yana gaya musu su taka dokar da Allah ya bayar a kan jini ke nan. (Farawa 9:4; Ayyukan Manzanni 15:28, 29) Amma Yesu ba zai taba gaya wa mutane su taka dokar Allah game da jini ba.—Yohanna 8:28, 29.

  • Da a ce manzannin suna shan jinin Yesu ne da Yesu bai ce “za a zubar” da jininsa yayin da yake magana game da hadayar da zai yi ba.—Matta 26:28.

  • Yesu ya yi hadaya ‘sau daya’ kawai. (Ibraniyawa 9:25, 26) Amma da gurasar da giyar tana juyawa ta zama jikin Yesu da kuma jininsa a duk lokacin da ake cin Jibin Ubangiji, da masu ci da sha sun rika mika hadayarsa a duk lokacin da suke ci da kuma sha.

  • Yesu ya ce: “Ku yi wannan abin tunawa da ni” amma ba “don hadaya da ni” ba.—1 Korintiyawa 11:24.

Wadanda suka yarda cewa gurasar da giyar suna zama jikin Yesu da kuma jininsa a lokacin cin jibi suna bin wannan koyarwar ne domin yadda aka fassara wasu ayoyi a wasu juyin Littafi Mai Tsarki. Alal misali a wasu juyin Littafi Mai Tsarki kamar Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa a Saukake, an yi kaulin Yesu yana cewa: “Wannan jinina ne.” (Matta 26:28) Amma za a iya fassara kalmomin Yesu kamar haka: “Wannan yana wakiltar jinina” ko kuma “Wannan yana alamtar jinina.” * A nan Yesu yana amfani ne da kwatanci kamar yadda ya saba yi.—Matta 13:34, 35.

Su wa ya kamata su ci gurasar kuma su sha giyar?

Idan Shaidun Jehobah suna yin Jibin Ubangiji, mutane kadan ne daga cikinsu suke cin gurasar da kuma shan giyar. Me ya sa?

An kafa “sabon alkawari” ta wurin jinin Yesu, kuma wannan alkawarin ya sauya alkawarin da ke tsakanin Allah Jehobah da kuma al’ummar Isra’ila ta dā. (Ibraniyawa 8:10-13) Wadanda suka sa hannu a cikin wannan alkawarin, ko yarjejeniya, suna cin gurasar kuma su sha giyar. Wadannan su ne Allah ya “kira su” ta hanyar mu’ujiza. (Ibraniyawa 9:15; Luka 22:20) Za su yi sarauta tare da Kristi a sama kuma Littafi Mai Tsarki ya ce mutane 144,000 ne kawai suke da wannan gatan.—Luka 22:28-30; Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1, 3.

Akasin wannan “karamin garke” da za su yi sarauta tare da Kristi, yawancinmu za mu zama a cikin “taro mai girma” da za su zauna a duniya har abada. (Luka 12:32; Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10) Ko da yake mu da za mu zauna a duniya ba ma cin gurasar kuma ba ma shan giyar, muna hada hannu da masu ci domin mu nuna godiyarmu saboda hadayar da Yesu ya yi a madadinmu.—1 Yohanna 2:2.

^ sakin layi na 3 Ka duba The New Cambridge History of the Bible, Kundi na 1, shafuffuka na 841.

^ sakin layi na 5 A kirgen kwanan wata, Yahudawa na yanzu suna sanin somawar watan Nisan ta wajen bin fitowar sabon wata, amma ba wannan salon ne aka bi a karni na farko ba. A maimakon haka, ana soma kirgen sabon wata ne da zarar an ga sabon wata a Urushalima, kuma hakan na iya zama kwana daya ko fiye da hakan bayan ainihin sabon watan ya fito. Wannan bambancin ne ya sa ba kowane lokaci ba ne ranar da Shaidun Jehobah suke tunawa da mutuwar Yesu yake zuwa daya da ranar Idin Ketarewa na Yahudawa na zamaninmu.

^ sakin layi na 14 Ka duba A New Translation of the Bible, na James Moffatt; The New Testament​—A Translation in the Language of the People, na Charles B. Williams; da kuma The Original New Testament, na Hugh J. Schonfield.