Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ba Ku Amfani da Gicciye a Sujjadarku?

Me Ya Sa Ba Ku Amfani da Gicciye a Sujjadarku?

 Mutane da yawa suna daukan gicciye cewa alamar Kiristanci ne. Ko da yake Shaidun Jehobah Kiristoci ne amma ba ma amfani da gicciye. Me ya sa?

 Dalili daya shi ne cewa Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa Yesu ya mutu a kan gicciye ba amma a kan itace ne. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya gargade Kiristoci su “guje ma bautar gumaka,” wato, yana nufin cewa ba za a yi amfani da gicciye a sujjada ba.​—1 Korinthiyawa 10:14; 1 Yohanna 5:​21.

 Mafi muhimmanci ma Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da kauna ga junanku.” (Yohanna 13:34, 35) Saboda haka, Yesu ya nuna cewa ba gicciye ne zai nuna wanda yake Kirista ba amma kauna ce za ta nuna wadanda suke mabiyansa na gaskiya.