Koma ka ga abin da ke ciki

A Ina Shaidun Jehobah Suke Samun Kudin Yin Ayyukansu?

A Ina Shaidun Jehobah Suke Samun Kudin Yin Ayyukansu?

 Gudummawar da Shaidun Jehobah suke bayarwa ne ake amfani da ita wajen yin ayyukan da muke yi a duk fadin duniya. a Akan saka akwatin ba da gudummawa a wuraren da muke taro. Ban da haka, akwai wasu hanyoyin ba da gudummawa a dandalinmu na jw.org/ha (ka duba: Gudummawa). A dandalin, mutum zai iya ba da gudummawa don ayyukan da muke yi a fadin duniya, ko a yankinsu, ko duka biyun.

 Shaidun Jehobah ba sa ba da zakka, kuma ba a gaya musu su ba da wani kaso daga cikin kudin da suke samu. (2 Korintiyawa 9:7) Ba ma karban baiko ko kudin shiga wurin taronmu, kuma wadanda suke yi wa mutane baftisma ko jawabin jana’iza, ko na aure da dai sauransu, ba sa karban kudi. Ba ma neman kudi ta wajen gaya wa mutane su ba mu zakka. Ba ma yin manyan taron tara kudi, kuma ba ma rokon mutane su ba da kudi. Kuma idan mutum ya ba da gudummawa, ba a sanar wa jama’a. (Matiyu 6:​2-4) Kari ga haka, ba ma saka tallace-tallace a dukan dandalinmu ko a littattafanmu don samun kudi.

 A dukan ikilisiyoyin Shaidun Jehobah, ana ba da rahoto kowane wata a kan kudaden da ake samuwa da yadda ake amfani da su. Ana hakan ne a taronmu da kowa yake iya halarta. Ana bincika rahotannin yadda ake amfani da kudade a kowace ikilisiya a-kai-a-kai, don a tabbatar cewa ana amfani da gudummawar a hanyar da ta dace.​—2 Korintiyawa 8:​20, 21.

Hanyoyin Ba da Gudummawa

 •   Akwatunan ba da gudummawa: Za ka iya ba da gudummawa ta wajen saka kudi ko cek a akwatunan ba da gudummawa da ke wuraren taronmu.

 •   Ba da gudummawa ta intane: A kasashe da dama, mutane suna iya ba da gudummawa ta wajen shiga shafin nan, “Ka Ba Shaidun Jehobah Gudummawa,” inda za su iya yin gudummawa ta yin amfani da katin ATM, ko su tura kudi zuwa asusun bankinmu, ko su yi amfani da wasu hanyoyi dabam. b Wasu Shaidun Jehobah sun tsara yadda za su rika ba da gudummawa kowane wata ta wadannan hanyoyin.​—1 Korintiyawa 16:2.

 •   Wasu hanyoyin ba da gudummawa: Wasu hanyoyin ba da gudummawa suna bukatar ka ya shiri da kyau ko ka nemi shawarar lauyoyi. Hakan zai iya sa ka samu ragin kudin harajin da ake biya, idan haka ake yi a kasarku. Mutane da yawa sun nemi karin haske a kan gudummawar da za su iya yi sa’ad da suke da rai ko kuma bayan sun rasu, kuma sun amfana daga yin hakan. Ka tuntubi Reshen Ofishin Shaidun Jehobah don ka sami karin bayani idan za ka so ka ba da gudummawa ta wadannan hanyoyin:

  •   ajiyar banki

  •   inshora da fensho

  •   fegi da gida

  •   hannayen jari

  •   wasiyya da ajiya

 Don samun karin bayani a kan hanyoyin ba da gudummawa da ake da su a yankinku, ka shiga shafin nan, “Ka Ba Shaidun Jehobah Gudummawa.”

a Wadanda ba Shaidu ba ma za su iya ba da gudummawa don ayyukanmu.

b Don karin bayani ka kalli bidiyon nan, Yadda Za A Ba da Gudummawa ta Na’ura.