Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah Suna Girmama Wasu Addinai Kuwa?

Shaidun Jehobah Suna Girmama Wasu Addinai Kuwa?

 Muna bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, “ku girmama dukan mutane”—ko da mene ne addinan su. (1 Bitrus 2:17) Alal misali, a wasu ƙasashe akwai ɗarurruwan dubban Shaidun Jehobah. Duk da haka, ba ma ƙoƙarin sa ’yan siyasa ko hukuma su hana ko kuma su ƙayyade aikin wasu rukunonin addinai. Ba ma zuga hukuma ta tilasta ɗabi’a ko kuma ra’ayin addininmu ga jama’a. Maimakon haka, muna girmama mutane yadda muke so su girmama mu.—Matta 7:12.