Koma ka ga abin da ke ciki

Kuna da Malamai da Ake Biya?

Kuna da Malamai da Ake Biya?

 Kamar yadda yake a Kiristanci na ƙarni na farko, Shaidun Jehobah ba su da bambanci na malamai da mabiya. Dukan waɗanda suka yi baftisma ministoci ne da suke wa’azi kuma da suke koyarwa. An tsara Shaidun a cikin ikilisiya na kusan mutane 100. Maza da suka manyanta a ruhaniya suke hidimar ‘dattawa.’ (Titus 1:5) Suna yin haka ne ba tare da ana biyansu hidimar da suke yi ba.