Koma ka ga abin da ke ciki

Ka Ba da Gaskiya da Yesu?

Ka Ba da Gaskiya da Yesu?

E. Mun ba da gaskiya da Yesu, wanda ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Mun ba da gaskiya cewa Yesu daga sama ya zo duniya kuma ya ba da kamiltaccen ransa hadayar fansa. (Matta 20:28) Mutuwarsa da tada shi daga matattu ya sa waɗanda suka ba da gaskiya gare shi su iya samun rai na har abada. (Yohanna 3:16) Mun kuma gaskata cewa Yesu Sarki ne yanzu da yake sarauta a Mulkin Allah a sama, ba da daɗewa ba zai kawo salama a dukan duniya. (Ru’ya ta Yohanna 11:15) Amma, mun gaskata abin da Yesu ya ce: “Uba ya fi ni girma.” (Yohanna 14:28) Saboda haka, ba ma bauta wa Yesu, don ba mu gaskata cewa shi Allah Maɗaukaki ba ne.