Koma ka ga abin da ke ciki

Ku ’Yan Ɗarika ne na Amirka?

Ku ’Yan Ɗarika ne na Amirka?

Hedkwatarmu ta duniyar tana ƙasar Amirka ne. Duk da haka, mu ba ’yan ɗarika na Amirka ba ne saboda waɗannan dalilan:

  • Wasu sun ce ɗarika rukuni ne da ta ɓalle daga wani kafaffen addini. Shaidun Jehobah ba su ɓalle daga wani addini ba. Maimakon haka, muna ganin mun kafa irin Kiristanci ne da aka yi a ƙarin na farko.

  • Shaidun Jehobah suna hidimarsu a ƙasashe fiye da 230. Ko a ina muke da zama, biyayyarmu ta farko ga Jehobah Allah ne da kuma Yesu Kristi, ba ga gwamnatin Amirka ko kuma wani gwamnati na mutum ba.—Yohanna 15:19; 17:15, 16.

  • Dukan koyarwanmu daga Littafi Mai Tsarki ne, ba daga rubutun wasu shugabannin addinai a Amirka ba.​—1 Tassalunikawa 2:13.

  • Yesu Kristi muke bi, ba wani shugaba ɗan Adam ba.​—Matta 23:8-10.