Kuɗin tafiyar da aikinmu ainihi daga gudummawa ne da Shaidun Jehobah suke bayarwa. Ba a karɓan baiko a taronmu, ko ushiri daga ’yan’uwa. (Matta 10:7, 8) Maimakon haka, ana ajiye akwatunan ba da gudummawa a wuraren taronmu domin in mutum yana so ya ba da gudummawa ya yi hakan.

Ba a sanar da sunayen waɗanda suke ba da gudummawa.

Dalili ɗaya da muke iya manejin kuɗinmu shi ne domin ba mu da shugabanni da muke biyansu. Ƙari ga haka, ba a biyan Shaidun su yi wa’azi gida gida, kuma wuraren bautarmu ba masu tsada ba ne. Dukan wani gudummawa da aka aika ofisoshin reshe na Shaidun Jehobah ana amfani ne da su a tallafa wa waɗanda bala’i ya ritsa da su, a taimakawa masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma masu ziyara, da kuma gina wuraren bautarmu a ƙasashe masu tasowa, sai kuma bugawa da tura Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai na Kirista.

Kowane mutum yana tsai da shawara ko zai ba da gudummawa domin bukatun ikilisiya ko kuma domin aiki na dukan duniya ko domin duka biyun. Kowace ikilisiya tana ba da rahoto a kai a kai na abin da aka yi da kuɗi.