Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Kuna Ba da Agaji a Lokacin da Bala’i Ya Auku Kuwa?

Kuna Ba da Agaji a Lokacin da Bala’i Ya Auku Kuwa?

Hakika, shaidun Jehobah suna taimakawa sa’ad da bala’i ya auku. Daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a Galatiyawa 6:10: “Bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba wadanda su ke cikin iyalin imani ba,” duk sa’ad da bala’i ya auku, muna taimaka wa Shaidu da kuma wadanda ba Shaidu ba. Muna kuma taimaka wa wadanda suke cikin matsalar wannan bala’in yadda za su sami ta’aziya kuma su yi wa Allah sujjada.—2 Korintiyawa 1:3, 4.

Yadda Ake Tsara Abubuwa

Sa’ad da bala’i ya auku, dattawan ikilisiya da ke a inda ya auku sukan yi kokarin su sada da dukan wadanda suke cikin ikilisiyoyi a yankin, su tabbata ba abin da ya same su kuma su san yadda za su taimaka musu. Bayan haka, sai dattawan su aika da rahoton abin da suka gani da kuma taimakon da suka yi zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke a kasar.

Idan abin taimakon da ake bukata ya fi karfin ikilisiyoyin da suke yankin, sai Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah su shirya su aika da sauran abubuwan da ake bukata. Wannan ya yi daidai da yadda Kiristoci na farko suka kula da juna a lokacin yunwa dā. (1 Korintiyawa 16:1-4) Ofishin Shaidun Jehobah a kasar yana nada kwamitin Kula da Agaji a Lokacin Bala’i don su tsara yadda za su tafiyar da ayyuka na taimakawa. Shaidu daga wasu wurare suna ba da kai su taimaka a wurin bala’in.—Misalai 17:17.

Yadda Ake Samun Kudin

Hanya daya da ake amfani da gudummawan kudi da ake aika zuwa ofishin Shaidun Jehobah shine don taimaka wa wadanda bala’i ya same su. (Ayyukan Manzanni 11:27-30; 2 Korintiyawa 8:13-15) Ana amfani da kudaden wajen taimakawa ne ba domin biyan kwamitin ba da agaji ko wadanda suka ba da kansu don taimakawa ba. Muna amfani da kudaden da ake bayarwa yadda ya dace.—2 Korintiyawa 8:20.