Koma ka ga abin da ke ciki

Kana Tsammanin Ka Sami Addini na Gaskiya Guda Ɗaya Ɗin nan?

Kana Tsammanin Ka Sami Addini na Gaskiya Guda Ɗaya Ɗin nan?

 Ya kamata waɗanda suke ganin muhimmancin addini su tabbata cewa wanda suka zaɓa ya gamshi Allah da Yesu. Idan ba haka ba, me ya sa suke cikin addinin?

 Yesu Kristi bai yarda da ra’ayin cewa akwai addinai da yawa, hanyoyi dabam dabam, waɗanda idan aka bi dukansu za su kai ga samun ceto ba. Maimakon haka, ya ce: “Ƙofa ƙarama ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu-samunta fa kaɗan ne.” (Matta 7:14) Shaidun Jehobah sun gaskata cewa sun sami wannan hanyar. Da ba haka ba, da sun nemi wani addini dabam.