Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Suke Zuwa Ƙofa Ƙofa?

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Suke Zuwa Ƙofa Ƙofa?

Yesu ya gaya wa mabiyansa su “almajirtarda dukan al’ummai.” (Matta 28:19, 20) Lokacin da ya aiki almajiransa na farko, Yesu ya gaya musu su je gidajen mutane. (Matta 10:7, 11-13) Bayan mutuwar Yesu, Kiristoci na ƙarni na farko sun ci gaba da baza saƙonsu ‘gida gida da kuma a sarari.’ (Ayyukan Manzanni 5:42; 20:20) Muna bin misalin waɗancan Kiristoci na farkon kuma mun ga cewa za mu fi saduwa da mutane ta wurin hidimar ƙofa ƙofa.