Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Mai Tsawun Kafa Shida

Littafi Mai Tsarki Mai Tsawun Kafa Shida

Kafin ka yi odar Littafi Mai Tsarki na rubutun makafi daga wurin Shaidun Jehobah, ka tabbata kana da wajen ajiye shi. Cikakken New World Translation​—da ake da su a harsunan Turanci, Spanish, da Italian na rubutun makafi​—sun kai manyan littattafai 20 zuwa 28 da ke bukatar wajen jera su da zai yi tsawun mita biyu (tsawun kafa 6 da inci 5) kenan!

Wasu irin Littafi Mai Tsarki ba sa bukatar wajen ajiyewa mai yawa haka ba. Note takers na’urorin rubuta kalmomin makafi yana taimaka musu su iya samun ƙarin bayyani cikin na’ura ta wurin amfani da wani sashe na na’ura da za a ijiye saƙonni ciki da yake da wani ƙaramin fin da ke ɗaga sama ya kuma sauka ƙasa don ya buga harafin rubutun makafi. Makafi ma za su iya samun kuma su saurari karatun littattafai ta wurin taimakon screen readers, da yake juya rubutu zuwa magana.

Ƙari ga haka, Shaidu sun shirya wata tsarin na’ura da ke juya wani rubutu zuwa rubutun makafi a harsuna da yawa. Bayan da aka shirya tsarin da ke ɗauke da bugu na harshen da kuma harafin makafi, sai tsarin ya iya juyar da shi zuwa rubutun Makafi. Yana kuma shirya littafin yadda zai kasance wa makafi da sauƙi su karanta. Wannan tsarin ya sa ya yiwu a buga littattafan rubutun Makafi, har da Littafi Mai Tsarki a rubutun makafi a dukan harshen da yake da harafin rubutun Makafi har da waɗanda ba sa amfani da harafin baƙaƙe.

Fiye da shekara 100 yanzu, Shaidu suna ta buga rubutun Makafi masu tushen Littafi Mai Tsarki wa Makafi, ana samunsu a harsuna 19 yanzu. Ko da yake makafi da suke son saƙon za su iya samun waɗannan littattafai kyauta, amma yawancinsu suna ba da kyautarsu ta yardan rai.

Kwanakin baya da aka fito da sabon littafi a taron gunduma na Shaidu, an gaya wa jama’a cewa za a iya yin odar da rubutun makafi bayan ɗan lokaci. Shekarar da ta wuce, reshen Amirka suka ka yi binciken ikilisiyoyinsu don su san makafi nawa za su halarci taron kuma wane tsari za su so na (rubutun takarda, na na’urar note taker, ko kuma na screen reader) ne.

An aika da rubutun makafi na kan takardar ne zuwa taron gundumar da suke da makafi, da su ma suka sami sababbin fitowa daidai da sauran mutane. An aika wa kowannensu ta wurin e-mail tsari na na’urar mako guda bayan taron gundumarsu.

Wata Mashaidiya ta ce: “Gata ce ta musamman mu sami littattafai daidai da sauran mutane. Zabura 37:4 ta ce Jehobah yana biyan bukatar ranmu. Ya yi hakan kuwa a wannan makon!” Wani kuma ya soma hawaye yana cewa: “Suna tunawa da ni. Na gode Jehobah da yake kula da mu.”