Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Daga Japan

Littafi Mai Tsarki Daga Japan

Shaidun Jehobah sun kafa sabuwar na’urar buga littattafai a madaba’arsu a Ebina, a kasar Japan don su iya tanadar da yawan bukatun Littafi Mai Tsarki wa mutane.

Da farko, an sami matsalar rashin wuta saboda girgizar kasa da tsunami da suka auku a kasar Japan, a ranar 11 ga watan Maris ta shekara ta 2011.

Duk da haka, an soma kaddamar da aiki a watan Satumba ta 2011. Kusan watanni uku, an buga fassarar Littafi Mai Tsarki ta New World Translation a harshen Sin da sabuwar na’urar.

Tsawon wannan sabuwar na’urar ya kai kafa 1,312. Na’urar tana buga littattafai, ta hada su, ta manne musu bango, ta jera su kuma ta saka su cikin kwalaye sai ta rufe su a jera su a kan katakan lodi.

Hadin Kai Ya Sa An Yi Nasara

Shiri da kuma tsara aikin da kyau ya sa an yi nasarar aikin. Alal misali, an kera akwatunan katako don a saka na’urar a ciki, aka rufe su da kuma loda su cikin manyan akwatunan karfe na kwashe kaya guda 34 kuma aka tura su daga Turai zuwa Japan.

An tura ma’aikata goma daga ofishin reshen Shaidun Jehobah da ke Amirka don su taimaka da aikin. Wasu sun yi watanni shida a Japan don koyar da ma’aikata a wurin yadda za su yi aiki da na’urar da kula da ita.

Sabuwar na’urar ta ja hankalin ma’aikatan madaba’o’in gwamnatin Japan. Saboda haka, a ranar 19 ga Maris, 2012, mutane fiye da dari daga wadannan wuraren suka zo zagaya reshen. Abin suka gani ya burge su kwarai.

Kafin su bar wajen, an ba kowannensu kofi guda na juyin New World Translation da aka buga da na’urar.

A yanzu rassa na Amirka da Brazil da Japan ne ke buga Littafi Mai Tsarki mai kaurin bango wa Shaidun Jehobah.

‘Aiki na Gaba Zai Fi Wuya’

Shaidu da ma’aikata da ba Shaidu ba da suka zo don aikin sun ji dadin yin aiki tare. Wani ma’aikaci da ba Mashaidi ba ya ce: “Kamar iyali kuke a gare ni.

A rana ta karshe na aikin, wani da ba mashaidi ba ya ce: “Aiki na gaba da zan yi zai fi wuya domin ba zai kasance da dadi irin na Watchtower ba!