Jerin bidiyoyin nan Ka Zama Abokin Jehobah da ke dauke da wakoki da kuma katun din su Kaleb da Safiya suna tashe sosai a duniya. Iyaye da kuma yara sun rubuto don su nuna godiyarsu a kan wadannan bidiyoyi dabam-dabam na wannan jerin. Ga misalan wasu kalaman da yara suka yi:

  • “Ina godiya don bidiyon nan ‘Ka Ji, Ka Yi Biyayya, Don Ka Samu Albarka.’ Ina kallon wannan bidiyon kowace rana tare da bebin robana.”—Zach, mai shekara 5.

  • “Sabobin wakokin nan sun nuna cewa Jehobah yana kaunata kuma yana so in yi masa addu’a a kowane lokaci.”—Mikariah, mai shekara 6.

  • “Na koyi yin biyayya ga iyayena da kuma yin tsabta. Na gode sosai da aka yi wannan bidiyon yaran.”—Nicole, mai shekara 8.

  • “Ina godiya sosai don wannan bidiyon. Ina farin ciki, ina jin dadinsa sosai kuma ina kaunarsa.”—Mckenzie, mai shekara 5.

  • “Ina son bidiyoyin nan Ka Zama Abokin Jehobah. Ina kallonsu kowace rana. Jehobah yana da kirki sosai da ya sa ku rika yin wadannan bidiyon.”—Ava, mai shekara 8.

  • “Ina jin dadin kallon bidiyoyin nan. Ina kokari na koyi dukan wakokin nan. Wadannan bidiyoyin nan son sa ina kaunar Jehobah.”—Devon, mai shekara 4.

  • “Ina dokin kallon bidiyon Kaleb na gaba! Ku ci gaba da yin wadannan bidiyon!”—Vance, mai shekara 8.