Koma ka ga abin da ke ciki

Kasar Estoniya Ta Ba da Lambar Yabo don “Wani Gagarumin Aiki”

Kasar Estoniya Ta Ba da Lambar Yabo don “Wani Gagarumin Aiki”

An zabi fassarar New World Translation of the Holy Scriptures a yaren Estoniya don gasar Language Deed of the Year Award na shekara ta 2014. A cikin littattafai da kuma shirin rediyo guda 18 da aka zaba, fassarar New World Translation of the Holy Scriptures a yaren Estoniya ta zo na uku.

Wata masanar ilimin harsuna mai suna Kristiina Ross ce ta zabi sabuwar fassarar New World Translation of the Holy Scriptures na yaren Estoniya da aka fitar a ranar 8 ga Agusta, shekara ta 2014. Ta ce wannan fassarar “tana da sauki da kuma dadin karatu,” kuma ta kara da cewa “aikin da aka yi a wannan littafin ya inganta aikin fassara a yaren Estoniya.” Wani farfesa na littattafan yaren Estoniya Rein Veidemann ya kira wannan sabuwar fassarar “wani gagarumin aiki.”

A shekara ta 1739 ne aka fara fitar da Littafi Mai Tsarki a yaren Estoniya kuma tun daga lokacin an fitar da fassara dabam-dabam na Littafi Mai Tsarki a yaren Estoniya. Amma me ya sa fassarar New World Translation ta zama “wani gagarumin aiki”?

Fassarar ta yi daidai. A cikin wani sanannen fassarar Littafi Mai Tsarki a yaren Estoniya da aka fitar a shekara ta 1988, an fassara sunan Allah “Jehoova” (wato, Jehobah) fiye da sau 6,800 a Nassosin Ibrananci (wato, Tsohon Alkawari). * Amma, fassarar New World Translation a yaren Estoniya ta saka sunan Allah fiye da haka ma. Kuma duk inda akwai hujjar saka sunan Allah a Nassosin Helenanci na Kirista (wato, Sabon Alkawari), mafassaran New World Translation sun yi hakan.

Saukin fahimta. Shin, fassarar New World Translation tana da saukin karatu da kuma fahimta kuwa? Wani sanannen mafassarin Littafi Mai Tsarki mai suna Toomas Paul ya rubuta a cikin wata jaridar Cocin Estoniya cewa fassarar New World Translation “ta cim ma manufar fassara mai kyau a yaren Estoniya.” Ya kuma kara da cewa: “Ina tabbatar muku cewa wannan ne karo na farko da aka cim ma wannan manufar.”

Yadda ake amfana daga wata fassara a yaren Estoniya

Mutanen Estoniya sun ji dadin wannan fassarar New World Translation sosai. An yi wani shiri na musamman na mintoci 40 a wani gidan rediyo a kan wannan sabuwar fassarar. Shugabannin coci-coci har ma da masu zuwan coci dabam-dabam sun yi odar wannan sabuwar fassarar. Wani babban makaranta a birnin Tallinn ta yi odar kwafi 20 na fassarar New World Translation don ta yi amfani da shi a wani aji. Estoniyawa suna son karatu kuma Shaidun Jehobah sun yi farin cikin fitar musu da fassarar littafi mafi kyau mai saukin karatu da ya yi daidai.

^ sakin layi na 5 Bayan Ain Riistan, wani shugaban New Testament Studies a Jami’ar Tartu ya bayyana yadda Estoniyawa suka soma kiran sunan nan “Jehoova,” sai ya ce, “A ganina, sunan nan Jehoova ya cancanta sosai a yau. Duk da yadda aka samo shi, ya kasance da ... muhimmanci sosai tun da dadewa. Hakika, Jehoova ne sunan Allah da ya aiko Dansa don ya ceci ’yan Adam.”