Koma ka ga abin da ke ciki

Aikin Fassara a Meziko da Amirka ta Tsakiya

Aikin Fassara a Meziko da Amirka ta Tsakiya

A Meziko da Amirka ta tsakiya, mafassara 290 da ke zaune a kasashe shida suna fassara littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki a cikin harsuna fiye da 60. Me ya sa suke irin wannan aikin? Suna hakan ne domin idan mutane suka karanta littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki a yare mai saukin fahimta a gare su, hakan yana ratsa zukatansu sosai.​—1 Korintiyawa 14:9.

Don su inganta fassarar da suke yi, an tura wasu mafassara da ke aiki a Bethel a Meziko zuwa wasu ofisoshin fassara a yankunan da ake yaren da suke fassarawa. Ta yaya hakan ya taimaka? Mafassara sun sami hanyar cudanya sosai da wadanda suke yin yarensu, kuma hakan ya taimaka musu su fassara littattafai a hanya mai saukin fahimta.

Yaya mafassara suka ji da irin wannan canjin? Federico, wani da ke fassara yaren Guerrero Nahuatl ya ce: “A duk tsawon shekaru kusan goma da na zauna a Birnin Meziko, na sadu da iyali daya ne tak da suke yarenmu. Amma yanzu, a garuruwan da ke kewaye da ofishin fassarar, kusan kowa yana yin yaren.”

Karin, wadda take fassara yaren Low German a ofishinmu da ke jihar Chihuahua a kasar Meziko ta ce: “Kasancewa da Mennonites ya taimake ni in yi amfani da kalmomin da mutane suka saba da su a fassarar da nake yi. Muna zama ne a wani karamin gari mu yi wannan aikin, kuma idan na duba ta tāga, nakan ga mutanen da za su amfana daga fassarar da muke yi.”

Neyfi, wadda take da zama a ofishin fassara a garin Mérida a kasar Meziko ta ce: “Yayin da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a yaren Maya, muna ganin kalmomin da suke ba wa mutanen wuya. Hakan yana sa mu yi amfani da kalmomin da suke da saukin fahimta.

Ta yaya mutanen da suke karanta littattafai da aka fassara suke amfana? Ka yi la’akari da wannan misalin: Elena wadda ’yar yaren Tlapanec ta yi wajen shekara 40 tana halartan taron Shaidun Jehobah, amma ba ta fahimci kome a wurin ba domin taron da Sifanisanci ake yi. Ta ce, “Ina zuwa taro domin na san cewa ya kamata in kasance a wurin.” Amma bayan da Elena ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki ta wajen yin amfani da littattafai da aka fassara da yaren Tlapanec, sai ta soma kusantar Allah sosai har ta yi baftisma a shekara ta 2013. Elena ta ce, “Na gode wa Jehobah da ya sa na fahimci Littafi Mai Tsarki.”