Yin Bidiyo a Harsuna da Yawa
An san Shaidun Jehobah sosai da aikin fassara. Zuwa watan Nuwamba na shekara ta 2014 mun fassara Littafi Mai Tsarki a harsuna 125. Ƙari ga haka, mun fassara littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki a harsuna 742. Aikin fassara da muke yi ya hada da fassara bidiyo. Zuwa watan Janairu na shekara ta 2015, mun fitar da bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? a harsuna 398, da kuma bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? a harsuna 569. Wane dalili ne ya sa muka soma yin wannan aikin, kuma ta yaya muka cim ma hakan?
A watan Maris na 2014, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ja-goranci ofisoshin Shaidun Jehobah a kasashe dabam-dabam a duniya su shirya bidiyo a harsuna dabam-dabam don taimaka wa mutane da nazarin Littafi Mai Tsarki.
Aikin fassara bidiyo ba cin tuwo ba ne. Da farko, mafassaran za su fassara bidiyon daga Turanci. Sa’an nan, za su zabi wasu da suke yin yaren don a dauki muryoyinsu a bidiyon. Bayan an dauki muryoyin mutane, masu aiki a dakin daukan murya za su gyara bidiyon da aka dauka da duk wani rubutun da ke cikin bidiyon. A karshe ana saka bidiyon a dandalinmu.
Wasu ofisoshin Shaidun Jehobah suna da dakunan daukan muryoyi kuma suna da kwararrun ma’aikata da suke yin wannan aikin. Amma, harsunan da ake fassarawa a wurare nesa da ofisoshin Shaidun Jehobah kuma fa?
A kasashe dabam-dabam, ’yan’uwa da suka iya amfani da na’urar daukan murya na tafi-da-gidanka suna zuwa aiki a wurare dabam-dabam. Wadannan kwararrun ma’aikata sukan kafa dakin daukar murya a wani ofishinmu ko Majami’ar Mulki ko kuma gidajen ’yan’uwa. Suna yin amfani da kwamfuta da makarufo da kuma na’urar daukan murya don cim ma wannan aikin. ’Yan’uwa da suka iya yaren suna ba da ja-gora a cikin dakin daukan murya kuma su tabbata cewa bidiyon ya yi daidai. Idan suka kammala wani bidiyon kuma suka tabbata cewa bidiyon ya yi daidai, ma’aikatan za su tattara kayan aikinsu su nufi wani wuri dabam da za su ci gaba da daukan muryoyin mutane.
Saboda wannan shirin, an fitar da bidiyo a harsuna da dama fiye da dā.
Mutane da yawa sun ji dadin kallon wadannan bidiyon. Kuma a wurare da yawa, bidiyonmu ne bidiyo na farko da mutane suka taba gani a yarensu.
Daya daga cikin harsuna da ke da bidiyonmu shi ne Pitjantjatjara, kuma mutane fiye da 2500 a Ostareliya ne suke yin yaren. An dauki su bidiyon yaren a cikin na’ura a garin Alice Spring a Northern Territory. Callan Thomas wanda ya taimaka wajen daukan bidiyon ya ce: “Mutane sun ji dadin bidiyon sosai. Sukan zuba idanu suna kallon wadannan bidiyon kuma suna tambaya ko akwai wasu bidiyon kuma. Babu littattafai da yawa a wannan yaren, saboda haka, a duk lokacin da suka kalli wani bidiyo ko kuma suka saurari wani abu a yaren, yana ratsa zukatansu sosai.”
Wasu Shaidun Jehobah guda biyu a Kamaru suna tafiya a cikin kwalekwale. Sun dan raba a kauyen mutanen da ake kira Pygmy kuma suka yi magana da sarkin kauyen, wanda shi malamin makaranta ne. Sa’ad da ’yan’uwan suka gano cewa sarkin yana jin yaren Bassa, sai suka nuna masa bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? a yarensa. Sarkin ya ji dadin bidiyon sosai har ya ce su ba shi wasu littattafai.
A wani kauye a Indunusiya, wani shugaban addini yana tsananta wa Shaidun Jehobah kuma ya kone duka littattafai da Shaidu suka rarraba a kauyen. Wasu a kauyen sun yi barazana cewa za su kone Majami’ar Mulki da ke kauyen. Bayan haka, wasu ’yan sanda guda hudu suka je gidan wata Mashaidiya kuma suka soma yi mata da iyalinta tambayoyi masu yawa. Sun je ne don su san abin da ke faruwa a Majami’ar Mulki, sai ta nuna musu bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? a yaren Indunusiya.
Bayan da suka kalli bidiyon, wani dan sanda a cikin su ya ce: “Yanzu na gane cewa mutane ne ba su fahimce ku ba.” Wani kuma ya ce: “Zan iya samun wannan bidiyon don in nuna ma wasu? Bidiyon ya ba da kwararren bayani game da ku.” Yanzu ’yan sanda a yankin ba sa tsananta wa Shaidun Jehobah kuma suna ba su kāriya.
Idan ba ku kalli daya daga cikin bidiyonmu ba tukun, ku yi kokari ku kalle su a yarenku.