Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Biki da wasu Bayanai don Asalin ’Yan Amirka a Birnin New York

Biki da wasu Bayanai don Asalin ’Yan Amirka a Birnin New York

Mutane da yawa suna tsammanin cewa Asalin ’Yan Amirka suna zama ne a kauyuka da ke wurare dabam-dabam na kasar. Amma Asalin ’Yan Amirka fiye da kashi saba’in suna zama ne a birane da ke kasar. A ranar 5 zuwa 7 ga Yuni, 2015, an yi wani biki da ake kira “Gateway to Nations” a birni mafi girma a Amirka, wato New York. * Sa’ad da wasu Shaidun Jehobah suka ji game da wannan bikin, sai suka soma shiri nan da nan don su halarta. Me ya sa?

Shaidun Jehobah suna fassara littattafai cikin darurruwan harsuna har da na Asalin ’Yan Amirka kamar yaren Blackfoot da Dakota da Hopi da Mohawk da Navajo da Odawa da kuma Plains Cree. Saboda haka, Shaidun Jehobah suka shirya wasu tabura da amalake na baza littattafai a wurin bikin don su nuna wasu cikin wadannan littattafan har da warkar nan You Can Trust the Creator!

Kari ga haka, akwai wasu sauti da kuma bidiyo na harsunan da aka ambata dazu a dandalinmu na intane. A bikin, Shaidun Jehobah sun saka wa bakin wasu daga cikin wadannan bidiyon da sauti, kuma bakin sun lura cewa yawancin abubuwa da aka yi a bikin da Turanci ko kuma Sifanisanci ne.

Mutane da yawa da suka halarci wannan bikin sun yi mamaki sosai don kokarin da muke yi wajen fassara littattafanmu zuwa harsuna da yawa na Asalin ’Yan Amirka da yadda muke koya wa mutane Littafi Mai Tsarki a birane da kuma kauyuka. Bayan wani ma’aikaci a bikin ya ji game da irin aikin da muke yi, sai ya gaya wa ’yan’uwa su zo su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kuma ya ce, “Ina sauraran zuwanku da kuma koyan Littafi Mai Tsarki!”

Wasu ma’aurata kurame da Asalin ’Yan Amirka ne sun zo wurin da muka baza littattafanmu, amma Shaidun ba su iya tattaunawa da su ba. Amma nan da nan, sai wata Mashaidiya wadda ta koyi yaren kurame ta zo wurin. Ta yi wajen minti 30 tana tattaunawa da ma’auratan kuma ta taimaka musu su sami wurin da ake taron yanki na Shaidun Jehobah a yaren kurame a yankinsu.

Shaidun Jehobah fiye da 50 ne suka yi wannan aikin koya wa mutane Littafi Mai Tsarki kuma bakin da suka zo wurin da Shaidu suka baza littattafai sun karbi littattafai fiye da 150 a wannan biki na kwana uku.

^ sakin layi na 2 Wani masani mai suna William K. Powers ya ce, wannan “biki ne da maza da mata da kuma yara suke waka da kuma rawa.”—Daga littafin Ethnomusicology, Satumba 1968, shafi na 354.