A Oktoba 2011, Shaidun Jehobah sun gabatar da wani tsarin gwada a gani don su sanar wa mutane saƙon Littafi Mai Tsarki ta wurin jera takardu da kyau a kan teburi da kuma cikin amalanke. Wannan gabatarwan a kudanci Manhattan ne, wurin da ya fi cika da mutane kuma a tsohon garin New York City.

An rarraba yankin zuwa kashi huɗu. Kowane yanki yana da wurare da yawa da waɗanda suke wucewa za su iya tsayawa su duba littattafan Littafi Mai Tsarki da aka jera su da kyau a kan teburi ko kuma a cikin amalanke da wani mai hidima na cikakken lokaci a yankin ke lura da shi. An yi yawancin jerin a ciki ko kuma kusa da wurin da motoci suke da yawa, da dubban mutane ke wucewa kowace rana.

A wuraren kuwa mutane za su iya samun amsoshin Littafi Mai Tsarki na tambayoyi da yawa. Mutanen da suke sauri za su ɗauki wani littafi da za su iya karantawa idan suka isa gida.

Littattafan akwai su a harsuna dabam dabam. Idan babu wani littafi a harshen da ake bukata, za iya yin oda kuma a dawo a karɓa bayan ’yan kwanaki.

Jama’a da masu mulki ma sun yi murna da wannan tsari na gwada a gani. Wani ɗan sanda ya ce: “Me ya hana ku yi tuntuni? Lallai kuna da abin da mutane ke bukata.

Wani mutum ya tsaya kwasam sa’ad da ya ga littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ya ce ya ga mutane a kan matakala suna karatun littafin kuma yana tunanin ina suka same shi. Yanzu ya ga wurin.

Wani matashi kullum yana shigewa zuwa wurin aikinsa a makonni shidan. Sai ya tsaya, ya ce, “ina bukatar taimako.” Waɗanda suke kula da teburi sun yi murna su taimaka masa. Sun ba shi Littafi Mai Tsarki kuma suka nuna masa yadda zai amfana daga ciki.

Mutanen da suke wucewa da suke da himma su kan tsaya a tattauna al’amura ta ruhaniya da su. A yanzu dai, wannan tsari na gwada a gani a Manhattan ya sa mutane sun iya karɓan mujallu 12,927 da littattafai 31,183.